Hukumar kula da ingancin kayayyakin masana’antu ta kasa (SON) ta ce, ta tura bukatar sake inganta dokokin hukumarta ga majalisar dokokin kasar domin ta samu damar zartar da hukuncin da ya kamata ga masu shigo wa da kayayyaki marasa inganci.
SON ta ce dokar da ake da ita yanzun, tana dakile ayyukanta don haka akwai bukatar ayi mata kwaskwarima.
“Mun riga mun mika wa majalisa bukatar gyaran kundin dokokin hukumarmu, wacce akwai bukatar samar da hukunci mai tsauri kamar zaman gidan yari ga wadanda suka aikata laifukan da suka shafi rashin samar da ingantattun kayayyaki a kasar,” in ji Darakta Janar na SON, Farouk Salim.
Salim wanda mataimakiyar darakta a hukumar, Mariam Samson ta wakilta, ta bayyana cewa dokar idan aka yi wa kwaskwarima za ta tabbatar da cewa masu sana’a da masu shigo da kayayyaki marasa inganci, baya ga yanke musu tara mai yawa, suma za su fuskanci hukuncin dauri a gidan yari bisa girman laifin da suka aikata.