Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya tashi daga kashi 20.77% a watan Satumbar 2022 zuwa kashi 21.09 a watan Oktoban 2022 a daidai lokacin da farashin kayan abinci ya kara tashi.
Hukumar ta kuma ce hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 23.72% a watan Oktoban 2022, daga kashi 23.34% a watan Satumbar 2022.
- Jaruman Nollywood Da Kannywood Sun Yi Wa Jos Tsinke Don Mara Wa Tinubu Baya
- Yau 15 Ga Nuwamba, Jihar Kaduna Ke Cika Shekaru 105 Da Kafuwa
Hukumar ta NBS ta bayyana hakan a cikin rahotonta na farashin masu amfani da kayayyaki (CPI) na watan Oktoba 2022 da ta fitar a ranar Talata.
Rahoton ya nuna kimar canjin farashin kayayyaki da ayyuka sun sauya.
“A kowane wata, farashin kayayyaki a watan Oktoba na shekarar 2022 ya kai kashi 1.24 bisa dari, wannan ya yi kasa da kashi 0.11 bisa na adadin da aka samu a watan Satumban 2022 (kashi 1.36). Adadin hauhawar farashin ya ragu da kashi 0.11 cikin dari.”
Matsakaicin bincike na watanni goma sha biyun da suka gabata ya kasance kashi 17.86 cikin dari, ya nuna habaka da kashi 0.91 bisa dari idan aka kwatanta da kashi 16.96 da aka samu a cikin Oktoba 2021.
Hukumar ta NBS ta dora alhakin hauhawar farashin kayayyaki daga kasashen waje, tsadar makamashi, hauhawar farashin abinci da dai sauransu.
“A kowace shekara, a watan Oktoban 2022, hauhawar farashin kayayyaki a birane yana kai kashi 21.63, kashi 5.11 sama da kashi 16.52 da aka samu a watan Oktoban 2021. A duk wata hauhawar farashin kayayyaki a birane yana kai 1.33 kashi a cikin Oktoba 2022, wannan ya ragu da kashi 0.12 ne idan aka kwatanta da Satumba 2022 (1.46%).”