A baya bayan nan ne aka kammala taron nune nunen kayayyakin abinci na Afrika na 2025 a birnin Nairobin kasar Kenya, inda kayayyakin kasar Sin suka ja hankalin mahalarta taron.
DagaDaga ranar Laraba aka kaddamar da taron nune nunen mai taken “sauya tsarin samarwa da amfani da abinci a Afrika domin makoma mai dorewa”.
Jibril Abubakar Ali, mai sana’ar sayar da sinadaran adana kayayyakin abinci a birnin Mombasa na kasar Kenya, ya ce ya yi farin cikin halartar taron nune nunen, saboda ya samu damar fahimtar sinadarai kamar na citric acid da kayayyakin abinci masu sitaci daga kamfanonin kasar Sin.
Ya kara da cewa, masu samar da kayayyaki na kasar Sin sun samu karbuwa saboda yadda suke samar da kayayyaki masu matukar inganci kan farashi mai rahusa, musammam ga kasuwar Afrika.
A nasa bangare, Edwin Masivo, shugaban kamfanin Global Exihibition a kasar kenya, kamfanin da ya shirya taron, ya alakanta karbuwar da sinadaran adana kayayyakin abinci da na dandano na Sin suka samu da kirkire-kirkiren da suka sanya su dacewa da bukatun mutanen Afrika.
Ya kara da cewa, masana’antar abinci ta Afrika na amfani da dabarun masu samar da kayayyaki na Sin, wajen samar da kayayyaki masu inganci. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp