Tun bayan kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi wa tsohon Sarkin Gobir wanda aka rage wa matsayi zuwa Hakimin Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa, hankulan ‘Yan Nijeriya sun yi matukar tashi saboda yadda matsalar tsaron da ake ta fama da ita a kasar ta kara kazancewa.
Kisan sarkin, ya nuna rashin ta ido da tsaurin idon masu aikata wadannan miyagun laifukan bisa yadda ake girmama sarakuna da martaba janibinsu.
- DSS Ta Kama Tsohon Editan BBC, Adejuwon Soyinka A Filin Jirgin Sama Na Legas
- Da Dumi-dumi: Tinubu Ya Maye Gurbin Bichi Da Ajayi A Matsayin Shugaban DSS
Duk da kisan gillar basaraken da ‘yan bindigar suka yi, kwana kadan da afkuwar hakan kuma suka sake komawa yankin Gobir suka sace fiye da mutum 150 da shanu akalla 1,000.
Daruruwan matasa a yankin sun gudanar da zanga-zanga a karshe bayan kashe hakimin yankin, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin jihar sanya dokar hana fita a Sabon Birni.
Da yake tabbatar da sace-sacen na baya-bayan nan ga Daily Trust, Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya ce abin takaici ne yadda ‘yan bingar suka koma bakin aikinsu a yankin kwanaki kadan bayan rasuwar hakimin.
Ya ce: “Abin da ya fi daure kai shi ne yadda wasu muhimman mutane a yankin za su iya shiga lambobin wayar ‘yan fashin har ma su rika tattaunawa da su. Me ya sa? Hakan na nuni da cewa an san inda ‘yan fashin suke.
“Mutanen yankin sun je tattaunawa da ‘yan fashi; yana nufin sun san inda suke. Me ya sa ‘yan fashi ke zuwa kasuwa cikin ‘yanci suna sayar da shanunsu a yankin?
“Me ya sa a yankin kimanin shanu 1,000 ‘yan fashi suka yi awon gaba da su. Shin shanun suna da fikafikan tashi ne? Hankalinmu fa ba zai dauki hakan ba. Ta yaya ‘yan fashin suka bi ta kauyuka da garuruwa ba tare da an lura da su ba?
“Suna kwashe shanun da suka sace zuwa cikin daji yayin da a lokaci guda kuma mazauna wasu al’ummomi a cikin gundumar suna cikin daji guda suna hakar zinare. A’a, lallai akwai wani abu da yake tafiya ba daidai ba. Mu gaya wa kanmu gaskiya. Dole ne mu zauna mu magance wannan matsala don makomar ‘ya’yanmu,” in ji Farfesa.
Dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkato mai wakiltar Sabon Birni (Arewa) Aminu Boza ya ce an sace mutane 151 a tsakanin Tsamaye da Sabon Birni.
“Kwana daya da rasuwar Sarkin Gobir, ‘yan bindigar sun sake kai hari kauyen Tsamaye, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance ba.
Haka kuma sun kai hari Kauyen Yanfaruna inda suka yi awon gaba da mutane 22 sannan suka je kauye na gaba suka yi awon gaba da mutane 11.
“Don haka, an yi garkuwa da mutane 192 kuma har yanzu suna hannunsu.
“Baya ga sace mutane, mun yi asarar sama da hekta 20,000 na fili ga ‘yan fashi. Sun hana mutanenmu yin noma shekaru da yawa yanzu. Sama da kashi 92 cikin 100 na dukiyoyinmu wadannan ‘yan bindiga sun salwantar,” in ji shi.
Boza ya yi zargin cewa babu jami’an tsaro a galibin wuraren da ‘yan fashin suka yi fama da su a Sabon Birni, wadanda suka hada da Kwanar Maharba, Turtsawa, Unguwar Lalle, Tagirke da Kwanar Tambazawa.
Ya ce: “Kwanar Maharba ita ce wuri mafi hatsari a cikin dukkan wuraren da na ambata. ‘Yan fashin na gudanar da ayyukansu a wannan wuri kusan kullum. A duk lokacin da za su je Sakkwato sai da wasu daga cikin mutanenmu suka canza hanyarsu ta Jamhuriyar Nijar, saboda ta fi tsaro. Ba mu da wurin binciken masu tsaro ko guda a kan wannan hanyar.
“An san wuraren da akasarin shugabannin ‘yan fashin suke. Misali Bello Turji yana zaune ne a Fakai kuma daga Fakai zuwa Shinkafi nisan da bai wuce kilomita uku ba. Halilu yana zaune a Kauyen Tsububu da Jummo Baki a Kauyen Gangara.
“Kwanaki uku da suka gabata na gana da mataimakin gwamnan Jihar Sokoto kuma tare muna kokarin tura karin sojoji 1,200 Jihar Sakkato kuma Sabon Birni zai samu karin jami’an tsaro nan da mako guda,” in ji dan majalisar.
Ya ce tura jami’an soji zuwa yankunan zai rage yawan ‘yan fashi da makami sosai.
Dan majalisar ya roki gwamnatin tarayya da ta saurari halin da mazauna unguwar Sabon Birni ke ciki.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Sakkwato, SP Ahmad Rufa’i, ya ce ‘yan sandan ba su samu rahoton sace-sacen mutane irin wannan ba, amma ya yi alkawarin gano hakan daga ofishin shiyya ta Sabon Birni. Sai dai har zuwa hada wannan rahoto ba mu samu karin bayani ba.
Har ila yau, tabarbarewar tsaron ba ta tsaya kawai a yankin Sakkwato ba, domin ko a yankin Jihar Neja, kwanan nan an kashe manoma 13 a Karamar Hukumar Shiroro. Yayin da kuma a Jihar Kaduna, ‘yan bindigar suka sace manoma bakwai tare da neman kudin fansa Naira miliyan biyu. Al’amarin ya faru ne a Unguwar Kankarami, dake Kauyen Unguwar Barde, kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar a yayin da wadanda ka yi garkuwa da su din ke aiki a gonarsu. Barayin sun yi awon gaba da manoman tare da kai su wani wuri da ba a bayyana ba.
Wani daga cikin daga cikin shugabannin al’ummar yankin Unguwar Barde da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da sace mutanen ya ce wadanda aka sace din duk maza ne. Shugaban ya bayyana halin da al’ummar yankin ke ciki, inda ya ce ‘yan bindigar sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan biyu, wanda ya fi karfin jama’ar kauyen.
“Mun yi matukar bakin ciki da faruwar lamarin.
Sace mutanen da aka yi mana a lokacin da suke aiki a gonarsu ya sa mu cikin rudani. Kudin fansa da ‘yan fashin ke nema ya zarce karfinmu na kudi saboda tabarbarewar tattalin arzikin da muke fuskanta,” in ji shugaban.
Ya kuma bayyana cewa idan ‘yan fashin suka hana shiga gonakinsu, mutanen kauyen za su yi wahala wajen ciyar da iyalansu.
“Ko da ‘yan fashin sun bukaci Naira miliyan 1, hakan ma ya fi karfinmu saboda muna fama da talauci,” in ji shi.
Kawo rubuta wannan labari dai babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma ‘yansanda dangane da lamarin. Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, ASP Mansir Hassan, lamarin ya ci tura.
Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Fusata
Sakamakon yadda matsalar tsaron ta kazance a wannan makon, shugabannin addini musamman mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa, Archbishop Daniel Okoh, sun nuna fusatarsu da yadda abin ya yi kamari musamman a mako dayan da ya wuce, inda suka fitar da wata sanarwa a karkashin Majalisar Hadin Kan Addinai ta Nijeriya (NIREC) game da lamarin.
Kungiyar ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya kawo karshen yawaitar ayyukan ta’addanci da sace-sace da kashe-kashen rayuka a Nijeriya, inda ta ce, lamarin ya wuce hankali.
Sarkin Musulmi da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), sun ce, akwai matukar damuwa game da karuwar rashin tsaro a kasar nan.
NIREC, a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun babban sakatarenta, Fr. Farfesa Cornelius Omonokhua, ta ce, kwanan nan ta samu rahoton kashe manoma da sauran mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kasar nan musamman mano 13 da aka kashe a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Majalisar ta kuma yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kula tare da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargin ayyukan ta’addanci ne, domin tsaro aiki ne na gama-gari ba na gwamnati kadai ba.
‘Yan Siyasa Ke Ta’azzara Abin Don Cimma Wata Manufa – Ngozi Okonjo-Iweala
A nata bangaren, Darakta Janar ta Kungiyar Bunkasa Kasuwanci ta Duniya, WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta soki ‘yan siyasar Nijeriya da amfani da rashin tsaro wajen yaki da ‘yan adawa domin cimma wata manufa ta siyasa.
Da take jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Nijeriya na shekarar 2024 a Legas ranar Lahadi, Misis Ngozi ta koka da cewa, amfani da rashin tsaro a matsayin makami, zai kara tsananta kalubalen kasar.
A jawabinta mai taken: ‘Mu’amalar zamantakewa domin inganta makomar Nijeriya a gaba’, Misis Ngozi ta jaddada muhimmiyar alaka tsakanin tsaro da cigaban tattalin arziki.
Ta soki ’yan siyasa kan haifar da rashin tsaro don lalata mutuncin abokan hamayyarsu, ba tare da la’akari da darajar dan’Adam ko asarar dukiya ba.
“Dukkanmu mun san cewa, ‘yan siyasa sun yi amfani da kawo kalubalen tsaro a kasarmu don dalilai na siyasa, wanda hakan ya haifar da wani bangare na kuncin rayuwa da muke ciki a yanzu.
“Muna da ‘yan siyasa da suka yi imanin cewa, hanya mafi kyau da za su bata gwamnatin abokan hamayyarsu, ita ce, tada zaune tsaye, ta yadda mutane za su debe kyakkyawan zato ga gwamnatin, ba tare da la’akari da cewa, matakin ka iya kai wa ga asarar rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba. Dole a dakatar da irin wannan tunani,” in ji Misis Ngozi Okonjo-Iweala.
A don haka, Misis Okonjo-Iweala, ta yi kira da a yi amfani da fasahar da ake da su wajen yaki da satar man fetur da kuma hukunta masu laifi, inda ta ce, dole ne a daina satar dukiyar kasa.
Tinubu Ya Yi Garambawul A Hukumomin Tsaro Na Sirri
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wani garambawul a manyan hukumomin tsaro na sirri inda a farkon makon nan ya maye gurbin tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) Ahmed Abubakar Rufa’i da sabon da ya nada, Ambasada Mohammed Mohammed.
Har ila yau, shugaban kasan ya kuma maye gurbin Shugaban ‘Yansandan Sirri, Yusuf Magaji Bichi Bichi tare da maye gurbinsa da Mista, nada Adeola Oluwatosin Ajayi.
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya ce Ambasada Mohammed ya yi fice a hidimar kasashen waje tun lokacin da ya shiga NIA a shekarar 1995.
A cewarsa, ya taba rike mukamai daban-daban, har ya kai ga kara masa mukamin darakta, sannan kuma an nada shi shugaban da ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa kasar Libya.
“Ya kammala karatunsa a Jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1990, ya yi aiki a kasashen Koriya ta Arewa da Pakistan da Sudan da kuma a fadar gwamnati da ke Abuja.
“Sabon Darakta-Janar na DSS, Mista Adeola Ajayi, da ya sami mukamin mataimakin darakta Janar na Hukumar. A lokuta daban-daban, ya taba rike mukamin darakta a jihohin Bauchi, Enugu, Bayelsa, Ribas, da Kogi,” in ji shi.
Ya ce sabbin nade-naden sun biyo bayan murabus din da shugabannin NIA da DSS suka yi.
A cewarsa, Shugaba Tinubu yana sa ran sabbin shugabannin tsaron za su yi aiki tukuru domin sauya hukumomin leken asirin biyu domin samun sakamako mai kyau da kuma samar da kwarewarsu wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan tare da hadin gwiwar hukumomi abokan aiki da kuma ofishin hukumar na kasa, da ofishin babban mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA).
An sanar da cewa shugaban NIA mai barin gado Ahmed Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa sabanin dalilin da ya bayyana na iyali.
Abubakar ya shaida wa manema labarai a daren ranar Asabar cewa ya yanke shawarar yin murabus ne saboda wasu batutuwa na kashin kansa, amma babu wani abu da ya shafi muzgunawa.
“Na mika takardar murabus dina kuma shugaban kasa ya amince kuma ya karba,” in ji Abubakar.
Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa wakilinmu cewa, bayan ziyarar da tsohon DG ya kai wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, an bukaci ya yi murabus ne saboda “sakaci da aka samu ta fuskar samun bayanan sirri” a lokacin zanga-zangar #Kuncin Rayuwa.
Wata majiya ta ce, “Ba wai kawai zanga-zangar kuncin rayuwa ba ce kawai, har ma da yadda zanga-zangar tasirinta, inda tutocin Rasha suka rika shawagi a wasu jihohi, sannan kuma masu zanga-zangar sun fito fili suna kiran sojoji su karbi mulki. ”
Wata majiyar kuma ta ce mai yiwuwa Abubakar ya gaza ne wajen samun wani tagomashi ne a wajen mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, wanda ofishinsa ne ke kula da hukumar.
A cewar majiyar, Abubakar ya shirya tafiya ne a daren ranar Asabar kuma ya je ya sanar da shugaba Tinubu wanda a lokacin ne aka ba shi shawarar yin murabus nan take.
Martani Kan Nadin Sabbin Shugabannin Tsaron
Wasu masana harkokin tsaro sun yaba da sauye-sauyen shugabancin hukumomin leken asiri, DSS da NIA.
Manjo Janar James Nyam (mai ritaya) ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa zabin da ya yi na sabon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, inda ya suffanta shi da wani abu da zai yi tasiri.
Ya yaba wa nadin da cewa yana da wani gagarumin ci gaba a yakin da kasar ke yi da makiya na cikin gida. Janar Nyam ya ce shugabannin tsaro da aka nada za su inganta yaki da miyagun laifuka saboda irin nasarorin da suka samu a aikin.
Ya ce, “Na san sabon Darakta Janar na DSS sosai a matsayin abokina, mun yi aiki tare da shi a Jihar Bauchi, inda shi ne darakta na jiha, ni ina matsayin kwamandan birgediya. Zan iya cewa shi kwararre ne, mai jajircewa akan aikinsa kuma yake da tsayawa kan abin da ya sa gaba.
“A aikin da muka yi tare da shi, mun samu damar dubawa tare da fatattakar ‘yan Boko Haram da sauran al’amuran barazana a jihar Bauchi tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, kamar yadda bayanai suka nuna.”
Na samu ilimi a aikin da muka yi da shi, wanda hakan zan iya cewa babban ci gaba ne. Zai fitar da sahihan bayanan sirri na cikin gida, kuma zan iya amincewa da cewa za a samu sakamako mai ban mamaki.”
Janar Nyam ya ce duk da cewa bai san sabon shugaban NIA ba, amma ya samu labari mai kyau game da shi.
“Ban san sabon shugaban NIA ba, amma mutane kadan da na yi magana da su ne suka bayyana ra’ayoyinsu game da mutumin. Don haka ina jinjina tare da jinjinawa hikimar shugaban kasa, C-in-C akan wadannan nade-naden. Tabbas za mu ga wasu ci gaba na ban mamaki!, ”in ji shi.
Game da daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a a cibiyar kula da harkokin tsaro ta kasa da kasa (IIPS), Dr Abdullahi Mohammed Jabi kuwa, cewa ya yi, maye gurbin shugabannin hukumar leken asiri wani ci gaba ne mai inganci domin tun lokacin da shugaban kasa ya gaji shugaban ma’aikatar ake ta zargin yin sulhu da gazawar hukumar leken asiri, don haka akwai bukatarsa a sake fasalin fannin.
Ya ce, “Abin da ake tsammani, babban abin da ke barazana ga kasar nan shi ne ta’addanci na tada kayar baya da kuma ‘yan fashi da makami, kuma da alama ana samun sulhu a wasu bangarori.
Da alama akwai gazawar tunani mai da wani lamari mai sarkakiya, kuma wannan, bisa ga ma’ana, ana ganin ba a samu wani ci gaba mai inganci a karkashin jagorancin da ya gada daga gwamnatin da ta shude ba.
“Yana kokarin gyara tsare-tsare a fannin tsaro da ingantattun al’amura don ba shi kyakkyawan bayani da ci gaba kan abubuwan da ke faruwa a wannan fannin. Hakan na da matukar muhimmanci; ta yadda zai kawo mutanen da ya yi imani da su, wanda hakan zai ba shi karin sakamako ta yadda ‘yan Nijeriya za su fara ganin gagarumar nasara a wannan fanni.
“Yana da lafiya sosai a cikin hukumomin leken asiri. Abu ne na nuna matukar farin ciki. Ana sa ran za a iya maye gurbin wasu shugabannin hukumomin tsaro da kwararrun mutane masu nagarta wadanda suka san ainihin mene ne al’amurran da suka shafi wannan fanni. ”
Har ila yau, wani kwararre kan harkokin tsaro, Iyke Odife, yayin da yake mayar da martani kan sabbin nade-naden da aka yi wa DG SS da DG NIA, ya ce zai sake fasalin tsarin tsaron kasar nan.
Ya ci gaba da cewa nadin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin rashin tsaro daban-daban da kuma bukatar sabbin dabaru don magance su.
Ya kuma bukaci wadanda aka nada da su kawo tarin ilimin da suke da shi don jure wa sabbin kalubalen da ake fuskanta domin amfanin kasa.
Sabon Darakta Janar Na DSS Kwararre Ne – Afunanya
An bayyana sabon darakta-janar na ma’aikatar harkokin gwamnati (DGSS), Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin jajirtacce kuma kwararren jami’in leken asiri wanda zai samu nasarori a ma’aikatar.
Da yake tsokaci game da nadin, Dr. Peter Afunanya, darakta, hulda da jama’a da dabarun sadarwa na DSS, ya ce “Mr Ajayi mai himma ne, mai juriya, wayayye, mai fafutuka da nazari. Ya zo a sabon matsayinsa tare da gogewa, iyawa da kuma kyakkyawar niyya.”
Ajayi ya yi aiki a 1990 a matsayin jami’in kadet kuma ya sami horo da yawa a fannoni daban-daban na gudanarwa, jagoranci tsaro, tunani da albarkatun dan ‘adam da sauransu daga ciki da wajen kasar nan.
Ya kuma rike mukamai da dama da suka hada da Daraktan Tsaro na Jiha (SDS) a jihohin Ribas, Bayelsa, Bauchi, Enugu da Kogi.
Shugaban Gwamnoni Ya Yaba Da Nadin Sabon Shugabannin Hukumar NIA, DSS
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak ya yaba da nadin manyan daraktocin hukumar leken asiri ta kasa (NIA) da DSS.
Gwamnan ya ce zaben gogaggen jami’in diflomasiyya, Ambasada Mohammed Mohammed, dan asalin garin Lafiagi a Jihar Kwara, ya jagoranci hukumar ta NIA ya bude wani kyakkyawan shafi a tarihin hukumar.
A wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, a daren jiya, AbdulRazak ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Tinubu bisa zabarn ma’aikacin diflomasiyyar dan asalin Jihar Kwara wanda har zuwa lokacin da aka nada shi shi ne shugaban tawagar Nijeriya a Sudan.
Abdulrazak ya kuma yaba da zabar Mista Adeola Ajayi, wani babban jami’in tsaro wanda ya jajirce wajen gudanar da ayyuka da dama a matsayin shugaban hukumar DSS.
Gwamnan ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su bada goyon baya ga sabbin wadanda aka nada, gwamnan ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da
ya bai wa sabbin daraktocin gaba daya hikimar samun nasarori da kuma inganta tsaron kasa.