Kada ki auna mijinki da girmamawar da wata mace ke samu daga nata mijin. Rayuwar aure tamkar riga ce, kowa da irin yadin da aka dinka masa.
Saboda gaskiyar magana ita ce, mijinki yana nuna soyayya da kulawa ta hanyarsa ba lallai ba ne ya yi irin yadda wani yake yi. Kuma wani lokaci, abin da mutane ke nuna maka ba cikakken labari ba ne.
- ‘Yan Makaranta Sun Kera Mota Mai Amfani Da Lantarki A Sakkwato
- Dalilin Ciwon Baya Yayin Goyon Ciki Da Hanyar Magance Shi
Ki rika kallon alherin da mijinki ke yi miki, ko da karami ne. Godiya ga kadan na iya janyo babba. Amma idan kika fara kallon “duba yadda mijinta ya saya mata mota”,
“Duba abin da mijinta ya wallafa a kanta.” Za ki fara jin tamkar na ki bai isa ba. Kuma hakan na iya rushe miki kwanciyar hankali.
Aurenki, ki dinga kulawa da shi da idon godiya, ba idon kwatance ba. Duk abin da ke na ki ya yi ko bai yi ba, Allah ne ya rubuta miki. Kiyaye kanki da daukar labarin wasu har ki fara jin naki bai da amfani domin wata na fakewa da murmushi ne, amma zuciyarta cike da kuka. Sannan baki da tabbacin gaskiyar al’amarin.
Da yawa matsalar da ma’aurata ke samu daga farko ita ce, shiga rayuwar aure da tunanin cewa aure gabadaya jindadi ne a ciki.
Da yawa sun dauki aure kamar rayuwar fim ko littafi da ake samun jin dadi dari bisa dari babu wani kalubale a tattare da auren.
Sai bayan sun yi auren sai a fara samun rashin fahimtar juna saboda ba a samu abin da ake tsammani a cikin auren ba.
Wannan na daga cikin musabbabin abin da ke kawo rashin fahimtar juna tsakanin ma’aurata.
Mafita a nan ita ce a matsayinku na ma’aurata kun shiga rayuwar aure da tunanin cewa za ku samu jin dadi dari bisa dari sai a ka samu akasin hakan, Ku da kan ku za ku iya sarrafa auren ku yadda kuke so ya yi armashi daidai gwargwado, ba wai sarewa za ku yi ba, ku fara fada da juna.
Jin dadin rayuwar aure ya danganta da yadda kuka dauki auren shi karan kan shi, Kuma za ku iya kwatanta irin rayuwar da kuke gani a fim ko karantawa a littafi, matukar akwai kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin ku.
Da fatan ma’aurata za su canja tunaninsu. Allah ya sa mu dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp