Waccan binckice na gidan jaridar ta Premium Times ya cigaba da cewa, wannan gwamnati ta Buhari, ta kere duk wata gwamnati da aka taba yi a wannan Kasa cikin jamhuriyar siyasa ta hudu wajen ciwo bashi, faro tun daga Shekarar 1999. (Premium Times, October 10, 2021).
A dai cikin jamhuriyar, ba a taba shaida inda runbum bashin Kasar yai mugun tsiri, tamkar irin yadda ya yi a karkashin mulkin Buharin Daura ba. Sai da ta kai ta kawo, bashin ketare da gwamnatin ta Buhari ta ciwo, ya ninka basukan da Kasar ta ciwo a lokacin Obasanjo da ‘yar’adua da Goodluck har sau ninki uku.
Ko mai Sanata Adeola zai ce game da wannan kididdiga, duba da karairayin da yai ta shirgawa a zauren Majalisa, sai ya gamsar da al’ummar Kasa cewa, sawun barawo ne kawai gwamnatin shugaba Buhari ke takawa game da sha’anin ciwowa Kasa mamakon bashi!!! Mhm, sai ya zo yanzu ya fitarwa al’ummar Kasar hakikanin barawon, da hakikanin sawun nasa!
Wancan gidan jarida na Firimiya ya ci gaba da fashin bakin cewa, lokacin da shugaba Obasanjo ya kama ragamar mulkin wannan Kasa a Shekarar 1999, ya sami adadin basuka na waje da ake bin Nijeriya da bai fi dalar Amurka biliyan ashirin da takwas ($ 28b). Ya yi iya yinsa wajen ganin ya durkusar da waccan akalar zaluncin bashin turawan yamma daga wuyayen ‘yan Kasa, inda ya zaftare adadi mai yawa daga basukan.
Ta tabbata cewa, lokacin da Obasanjo zai bar mulkin wannan Kasa a Shekarar 2007, duka duka basukan ketare da suka rage ake bin Nijeriya bai fi dalar Amurka biliyan biyu ($ 2b) ba. Wanda wannan namijin kokari ya samu ne sakamakon wasu abubuwa biyu da aka lasafta ya yi su, a baya cikin wannan rubutu.
Abu na farko, ya tashi haikan ne wajen biyan bashin da ake bin Kasar. Na biyu, yakai gwauro ya kai mari, sama da sauran shugabannin Afurka, na son ganin an yafewa wannan Kasa mummunan kunzumin katin bashin da aka coga mata.
Yayinda gwamnatin ‘yar’adua ta zo, ta kara bashin dalar Amurka biliyan guda ne da digo 39 ($ 1.39b) kacal akan wanda ta tarar. A lokacin da Goodluck ya amshi sitiyarin mulkin Kasar kuwa, ya kara adadin dalar Amurka biliyan uku ne da digo 3 ($ 3.8b) akan wanda ya riska. Duk da haka, cikin Shekarar 2015 lokacin da gwamnatin Goodluck ta zo karshe, daukacin basukan da Kasashen ketare ke bin Nijeriya bai wuce dalar Amurka biliyan bakwai da digo 3 ($ 7.3b) ba.
Wani abin takaici gami da firgicin shi ne, yayinda shugaba Buhari ya dafe akalar mulkin wannan Kasa da Shekara biyar kacal, bashin ketare da Kasar ta hadiyo, ya ninka basukan da gwamnatocin Obasanjo da na ‘yar’adua da kuma na Goodluck suka ciwo har sau ninki uku. Kididdigar ta wassafa cewa, cikin Shekarar 2020 kawai, bashin ketare da ake bin wannan Kasa sai da ya riski adadin dalar Amurka biliyan ashirin da takwas da digo 57 ($ 28.57b). Inda za a ga dalar Amurka biliyan ashirin da daya da digo 27 ($ 21.27b) ne cifcif suka karu akan adadin kudaden da gwamnatin Buharin ta riska daga gwamnatin Goodluck na dalar Amurka biliyan bakwai da digo 3 ($ 7.3b).
Dambarwar Bukola Saraki Da Baba Buhari
Cikin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu, an rika samun afkuwar rashin fahimtar juna tsakanin bangaren zartaswa na gwamnati, da kuma bangaren shugabancin zaurukan Majalisun Wakilai da na Dattijai daga lokaci zuwa lokaci. Sai dai, a fili ne yake cewa, sau da yawan lokuta, daga manyan dalilan da ke afkar da irin wadancan cece-kucen a tsakanin bangarorin biyu, bai wuce yunkurin masu zartaswa na jefa zaurukan majalisun biyu cikin kwarmin aljihunsu ba. Sai a wayigari, duk wani son zuciya da kauce ka’ida da shugabanni za su zo da shi a Kasa, sai a rasa masu taka musu burki ke nan ruwa ta sha!!!.
Bayan Obasanjo ya dare bisa karagar mulkin wannan Kasa cikin Shekarar 1999, maimakon gwamnatinsa ta sakarwa ‘yan Majalisar Dattijai mara su nada wanda suke so ya jagorance, sai kawai ta daurewa Chief Eban Ewerem gindin zama shugabansu. Hakan, ya dagula lamuran siyasar Kasar ainun, musamman ma zauren majalisar, wanda a karshe sai tuge shi ne suka yi daga kujerar jagorancin nasu, tare da nada wanda yake shi ne zabinsu, wato Sanata Chief Chuba Okadigbo.
Shi ma bangaren zauren ‘yan majalisun wakilai a lokacin Obasanjon, karkashin jagorancin Rtd Hon. Ghali Umar Na’abba ba su kwashe da dadi ba, kasantuwar tsohon Sifika, Salisu Buhari, mai karyar takardun ilmi, shi ne zabin bangaren masu zartarwar gabanin a tsige shi. Irin wannan danbarwa ta son zuciya da ta rika faruwa, na, sai wane ne zai jagorà nci zauruka biyu na majalisun taraiyar wannan Kasa, daga son zuciyar shugaban kasa da ‘yan kanzaginsa, ya ci gaba da jan linzaminsa har zuwa lokacin mulkin Baba Buhari, 2015-2023.
Dalilai na fili da na boye, sun rika ta da jijiyar wuyar gwamnatin Buhari da sauran ‘yan korenta cewa, sai shugabancin Sanata Bukola Saraki ya taba kasa, tare da yunkurin maye gurbinsa da Sanata Ahmad Lawan dan mutan Yobe.
Gudun sauka daga doron mauri’in da muke ta sukuwa birbishinsa tsawon Satika, a fili ne yake cewa, lokacin shugabancin Sanata Saraki, ba su ba da kai bori ya hau nan da nan ba ga bangaren masu zartaswa, idan an zo batun laftowa Kasa bashi, tamkar irin yadda sabon shugabancin Sanata Lawan ya dinga yi dare da rana, a na ta kandamowa wannan Kasa bashi daga gida da waje, sai sa’adda gwamnatin Buhari ta shawo gangara ne ma Lawan din ya fara wani fargar jaji marar fa’ida, na yunkurin fara taka burki ga bangaren na zartaswar game da sabgar ciwo bashin.
Akwai wani lokaci da Sanata Saraki da abokanan aikinsa suka ki amincewa da wata bukatar ciwo bashi da gwamnatin Buhari ta yi, na zunzurutun kudi dalar Amurka biliyan 29 da digo da digo 9 ($ 29.9bn). Wani abin takaicin ma shi ne, lokacin da aka gabatar musu da bukatar ciwo bashin da farko, sai aka ki faiyace musu abinda ma za a yi da bashin idan an amso. Shin, ta yaya ne ma bangaren zartarwas zai rika yadda wadanda ba ‘yan amshin shatansu ne za su rika shugabantar majalisar ba? A farko farkon mulkin na Buhari, da daman jama’ar wannan Kasa na kallon su Saraki ne da makiya son ci gaban al’umar Kasa, sai daga baya ne da aka yi walkiya halin kowa ya fito da shi waje kar!
Inda-Inda Game Da Sha’anin Ciwo Basukan
Wani lokaci a Kasar, sai mutum ya ji cewa, za a ciwo bashi iri kaza, da zimmar yin aiki iri kaza da bashin. Bayan wasu lokuta kuma, sai a ji manyan jami’an gwamnati na fadin, ai tuni ma an riga an ware kudaden da aka kafa hujjar ciwo wannan bashi da su. Gwari gwari, akwai wani lokaci da gwamnatin ta Buhari ta nemi ta kara ciwo wani bashi na dalar Amurka biliyan 22 da digo 6 ($ 22.6bn), tana mai cewa, akwai wasu aiyuka ne da gwamnati ta gaje su tare da son kammala su. Wadancan aiyuka kuwa sun hadar da;
-Gada ta biyu ta jihar Niger.
-Babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.
-Babbar hanyar Abuja zuwa Kano.
-Hanyar gabashi zuwa yammacin kasa, sannan sai
-Tashar wutar lantarki ta Mambila.
Kafin mu zo ga batun shin irin wadancan aiyuka sun cancanci a rika antaya musu irin wadannan makudan biliyoyin kudade? Zai yi kyau a fadawa mai karatu mene ne inda inda cikin wannan yunkuri na gwamnatin Buhari wajen kara ciwo bashi na irin wadannan madudan daloli?.
Bayan wani lokaci da gwamnatin taraiya ta tasamma ciwo wancan bashi da sunan kammala gadaddun aiyuka biyar (5), sai kuma aka ji ministan yada labarai na gwamnati, wato Lai Muhammed, na bugun kirjin cewa, tuni gwamnati ta ware kudi har kimanin naira biliyan guda da digo 5, don kammala wadancan aiyuka biyar da aka lasafta a sama.
An ciwo bashi, an kuma ce tuni ai da ma an ware kudaden karasa aiyukan tun a cikin Shekara 2018. To ina batun Tashar Lantarki ta Mambila ya karke?. Wane karairayi ne manyan jami’an gwamnati ba su yi ba, su bugi kirji su ce, ai ma tuni an kammala aikin tashar wutar, can kuma sai a sami wani sabon babban jami’i na gwamnatin, sai ya fito ya ce karya ne ba a ma ko share wurin da za a yi aikin tashar ba! Ke nan ma, ba a na maganar an zuba kudaden basukan ne a inda ba su cancanta ba, a’a, magana ma ake yi ta, ina ne hakikanin wuraren da aka shinfide basukan a cikinsu?.
Ya kamata fa mu dawo haiyacinmu game da madudan basukan da shugaba Buhari da sauran gwamnoni a Kasa masu barin gado suka ingizo mana, da kuma sabbin zababbun gwamnonin da za su gaje su! Lamarin basukan ba abu ne ba na wasa, tun da a ta-bakin wasu masana da kwararru, lallaftun basukan da shugaba Buhari ya jibgowa wannan Kasa, sai an shafe shekaru akalla talatin (30yrs) a na biyansu dare da rana. Ba cin bashin kai-tsaye ne laifi ba, a’a, mene ne hakikanin abinda aka yi da daukacin kudaden? Shin, an sanya kudaden ne ma a inda suka dace? Wace sahihiyar hanya ko hanyoyi ake bi a yau, wadanda za su nuna an doshi hanyar biyan basukan ta hakika?.
Ga ra’ayoyin masana da sauran manazarta, kuskure ne a rika raraka kudade ga aiyukan titina da gadoji da makamantansu, amma misalin aikin wutar lantarki, idan da akwai kyakkyawan shiri a kasa, ya cancanci a kyalaya madudan kudade ciki, kasantuwar akwai yadda za a yi su biyawa kansu basukan. Amma abin takaici karkashin mulkin na Buhari, an lafka tiriliyan kaza cikin lamarin lantarkin amma a banza a ta bakin gwamna ElRufa’i. Ya kara da cewa, irin wannan dalili na tozartar da kudaden, na daga abinda ya sanya gwamnatin ba ta Buhari ba ta da wani kwarin gwiwar bincikar madudan kudaden da gwamnatin Obasanjo ta kashe ko ta antaya cikin sabgar wutar!!!. Ina ke nan za a sa kai cikin wannan Kasa game da batun basukan, tun da hatta ma cikin sabgar da za a sa kudaden bashin masu ma’ana su haihu, an sa amma sun mutu murus? Karkashin wane shugaban kasa ne ko gwamna, sa’adda za a fara daukar sahihiyar hanyar biyan wadannan basukan gida da na daji da za su fara yi mana bake-bake a cikunanmu nan da wasu shekaru?. Cuta dai kam an cutar da mu!!!.
Zai yi kyau mu gangara zuwa ga wasu daga jihohinmu na Kudanci da kuma Arewacin wannan Kasa, don hakaito wasu daga irin nasu burunkaduwar badakalolin basukan da suka kaikaice suka laftawa jama’ar jihohin nasu musamman mutane raunana wadanda duk wuya ko rintsi ba su da wani wajen gudu ko yin hijira a duk sa’adda babbar annobar basukan da ke tafe ta mamaye Kasa!