Kimanin ‘ya’yan jam’iyyar APC su 1,000 ne suka fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Kano.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce, ‘ya’yan jam’iyyar APC sun sauya shekar ne a kananan hukumomin Tofa da Ghari inda shugaban jam’iyyar na jihar, Dr. Hashimu Dungurawa ya karbe su.
- Gobara Ta Ƙone Gidan Kakakin Majalisar Zamfara
- Amurka Ta Kitsa Shirin “Volt Typhoon” Ne Da Nufin Bata Sunan Wasu Kasashe
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ta kara zage damtse domin samun nasara a zabukan kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa a jihar Kano.
Jam’iyyar ta yi amfani da wannan dama wajen kaddamar da yakin neman zaben shugaban karamar hukumar gabanin zaben.
Dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Tofa a jam’iyyar NNPP, Yakubu Adis, da takwaransa na Ghari, Hashimu Mai Sabulu, a yayin bikin sun nuna kwarin gwiwa game da samun nasara a zaben da ke tafe.
Dukkan ‘yan takarar biyu sun bayyana jin dadinsu da samun sabbin magoya inda suka ce, wannan babbar nasara ce ga jam’iyyar NNPP.