Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Kira Ga Gwamnatin Jihar Zamfara

by
3 years ago
in SHARHI
5 min read
‘Darussan Sace Tagwayen Amare A Zamfara’
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Da farko dai ina farin ciki da samun wannan damar a matsayina na cikakkiyar ‘yar kasa mai ‘yancin magana da cewar ya dace na yi tsokaci akan wani abu da yake damuwar al’ummar wannan kasa.

Na san cewar, labarin satar ‘yan mata guda biyu tagwaye wato Hassana da Hussaina ya kai ko’ina a kasar nan, duk da cewa Alhamdu Lillahi cikin yardar Allah an samu nasarar karbar su, Sai dai kuma duk da hakan, ba ta nan gizo ke sakar ba, yadda aka yi aka fito da su shine lokacin da Mai girma Sanata Kabiru Marafa ya ba da tallafin sa na Naira milyan shida da sauran kudaden da al’ummar Nijeriya suka tallafa inda aka hada Naira milyan goma sha biyar, sai aka kira wadanda suka yi garkuwar da su tagwayen aka sanar masu da cewa kudin sun cika kamar yadda suka ce a biya su kafin su kai ga sakin tagwayen, bayan an sanar da su cewa kudin sun cika sai suka ce to a jira su za su kira don a kai masu kudin.

Bayan kamar awa uku sai suka kira wayar Ibrahim mijin yayarsu wanda ake sasantawar da shi, suka ce a dauko kudin azo wani gari da ake kira Gurbin-Burai inda kwanaki masu garkuwa da mutanen suka yi kashe-kashe da kone-kone suka ce idan an isa garin a kira su, kafin su Ibrahim su isa garin masu garkuwa da tagwayen suna ta kiran su a waya cewa mi yasa har yanzu ba su iso ba? sun gaji da jira, su fa zasu iya kashe tagwayen suyi tafiyar su, sai dai azo a dauki gawarwakin su, Ibrahim dai ya yi ta basu haduri yana ce masu ku kara hakuri mun kusan isowa.

Labarai Masu Nasaba

Matsalar Tsaron Jihar Kaduna: Yadda Al’amura Ke Kara Dagulewa

Ko Babban Taron APC Da Na PDP Danjuma Ne Da Danjummai?

 

Bayan su Ibrahim sun isa garin na Gurbin-Burai suka kira masu garkuwan suka fada masu cewar sun iso garin, sai suka ce to daga nan su biyo ta wani kauye da ake kira Dumburum daga Dumburum daji za’a shiga, to su Ibrahim sai suka ajiye motar su suka nemi mashina guda uku, sai masu garkuwan suka kira waya suka ce ai mun ganku ku taho garin na Dumburum zamu fada maku hanyar da zaku bi ta kawo ku cikin daji inda muke, jama’a kunga wannan ya nuna cewa akwai masu yiwa ‘yan bindigar leken asiri ko ta ina a cikin wadannan garuruwa na jihar Zamfara.

Daga garin Dumburum su Ibrahim sun yi tafiya kamar tsawon kilo mita 15 a cikin daji suna cikin tafiya kawai sai suka fara ganin mutane da bindigogi suna ta bullowa wanda yawansu ya kai kusan mutum dari da hamsin, kuma kowa yana rike da bindiga kirar AK47 ana cewa su dakata a wurin, sai su Ibrahim suka dakata, suka sauka daga kan mashina, da ma su uku ne, da shi Ibrahim mijin yayar su, da wanda zai auri Hussaina, da babban yayansu, sai Ibrahim ya dauko kudin ya ajiye a gabansa wanda aka zuba kudin a cikin jaka guda biyu, ‘yan bindigar sun gewayesu a tsakiyar daji, bayan kamar mintuna biyu sai ga shugaban ‘yan bindigar ya bullo tare da tawagarsa rike da manyan bindigogi tagwayen suna bayansu

 

Haka shugaban barayin ya matso har kusa da Ibrahim inda kudin suke ajiye a cikin jaka a ‘kasa, bai ce masa komai ba sai yayi umarni da wasu yaranshi guda biyu su bude jakunkunan su kirga kudin, bayan sun kammala kirga kudin gaba daya sun cika milyan 15, sai Shugaban ya ce, a mayar da kudin cikin jaka a daure, da akayi hakan, sai  ya tsuguna a gaban kudin ya debi kasa da hannunshi ya watsa akan jakakkunan kudin, sai ya mike tsaye ya hau kan jakunkuna kudin da kafafun sa, ya daga kanshi sama yana ta karanta wasu ‘dalasimai irin na tsafi, yana tayi har kusan kamar mintuna 2 sai ya saukar da kanshi kasa, ya kuma sauka daga jakar kudin ya ja da baya, sai ya yi umarni ga yaranshi da su dauki kudin, sai suka dauka,  daga nan sai ya kalli Ibrahim ya yi dariya ya ce, sannun ku da zuwa ashe kuna son kannen ku.

 

Sai Ibrahim ya amsa masa, da cewar ai ba wanda baya son kannen shi ya Shugaba, daga nan sai ya bada umarni da a kawo tagwayen ya mikasu ga Ibrahim ya ce, su juya su tafi kar su kuskura su juya baya, Ibrahim amsa dace wa mun gode oga, shine suka dauko tagwayen suka iso har kauyen Gurbin-Burai inda motarsu take ajiye, daga nan sai Ibrahim ya fara kiran waya suna sanar da ‘yan uwa da wadanda suka tallafa cewa tagwayen sun samu kubuta lafiya.

 

Jama’a wannan shine bayanin abinda ya faru dangane da yadda aka je aka karbo tagwayen.

Abinda binciken mu ya tabbatar mana shi ne an jima ana bibiyar tagwayen domin ayi garkuwa da su, mutane da dama suna da hannu a cikin garkuwa da ‘yan matan. Nazarin da muka yi a kai shine  su wadannan masu aikata laifin garkuwa da mutane sun bullo da wata sabuwar hanyar yin garkuwa da mutane ta hanyar bibiyar mutanen da suke mu’amala da dandalin sada zumunta na zamani musamman wadanda suke watsa hotunan su a social media, masu garkuwan suna la’akari da farin jinin wanda yake social media da yawan jama’ar da suke tare da shi wanda idan sun yi garkuwa da shi dole za a biya su kudi.

 

Kun ga wadannan tagwayen babban abinda ya yi sanadiyyar jefa su cikin wannan bala’i shine saka hotunansu da suke yi a social media da irin yadda ake kambama su, wadanda suka yi garkuwa da su sun dauki lokaci mai tsawo suna bin diddikin su har zuwa ranar da tagwayen suka ziyarci garin Mahaifinsu domin su raba katin aurensu. Garin kauye ne, a daren ranar da za ayi garkuwar da su, isar su kauyen ke da wuya sai suka ta fi yawo, kuma duk inda suka wuce sai an nuna su, da dare ya yi misalin karfe 11 da wasu mintuna aka je gidan kawarsu da suka sauka zasu kwana aka sace su gaba daya, har da kanin mijin kawar tasu, da ita kawar tasu aka tafi dasu daji.

Muna nazarin ayyukan masu garkuwa da mutane da dabarun su, mun sani cewa idan masu garkuwa da mutane sun kama mutum biyu ko sama da haka, to ba sa yarda su saki daya ko biyu su bar wani, a’a sai dai su sake su gaba daya, to amma wannan sun kama su gaba daya, sai suka saki tagwayen sauran kuma basu sake su ba, wannan zai tabbatar maka da cewar masu garkuwar sun yi karfin da ya wuce tunanin duk wani mai tunani ko hasashe da nazari, kuma wannan babban kalubale ne ga gwamnatin Nijeriya, mahukunta sai sun yi da gaske idan kuma ba haka ba masifar zata mamaye kasu jihohi da dama a Nijeriya

 

Daga karshe ina kira ga ‘yan mata da maza masu yada hotunansu a kafofin sada zumunta kuma suke da dimbin masoya da suyi taka tsantsan, sannan su kiyaye sirrin tsaron kawunan su, ku bar bayyana inda zaku je idan zaku yi tafiya, saboda bayyanawar  ba karamin hatsari ne mai girma a irin wannan lokaci da kuma halin da muka tsinci kan mu, a rika batar da kafa idan za ayi tafiya ko kuma za a dawo daga tafiya.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Wutar Daji Babban Bala’i Ce  Ga Al’umma —Farfesa Jaro

Next Post

Bakuwarmu Ta Mako: Barista Bilkisu Ibrahim Suleiman

Labarai Masu Nasaba

Matsalar Tsaron

Matsalar Tsaron Jihar Kaduna: Yadda Al’amura Ke Kara Dagulewa

by Bello Hamza and Shehu Yahya
1 month ago
0

...

Taron

Ko Babban Taron APC Da Na PDP Danjuma Ne Da Danjummai?

by Bello Hamza and Idris Aliyu Daudawa
2 months ago
0

...

Masoya

Bikin Ranar Masoya Ta Duniya A Mizani

by
3 months ago
0

...

Noman Rogo

Kokarin CBN Wajen Sake Farfado Da Noman Rogo A Nijeriya

by
3 months ago
0

...

Next Post

Bakuwarmu Ta Mako: Barista Bilkisu Ibrahim Suleiman

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: