Mabiya addinin Kirista a Jihar Filato sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Litinin, suna nuna rashin jin daɗinsu game da kisan gilla da aka yi a ƙaramar hukumar Bokkos, da Riyom da Bassa.
A yayin zanga-zangar, mabiyan sun yi kira da a dakatar da wannan mummunar ta’addanci, wanda suka bayyana a matsayin take hakkokin bil’adama da kuma kawo tarnaki ga zaman lafiyar ƙasa.
- Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa
- Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
Zanga-zangar ta fara daga mararrabar Favwei, ta tafi ta shataletalen PRTV a Rayfield sannan ta ƙare a gidan gwamnatin Jihar Filato, inda Gwamna Caleb Mutfwang da mataimakinsa, Ngo Josephine Piyo, suka karɓi mabiya zanga-zangar.
An shaida cewa wannan zanga-zangar na zaman ta biyu ne da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) da kuma inuwar Jagororin Addinai.
Jagororin cocin sun bayyana cewa wannan harin ba wai rikicin ƙabilanci bane, sai dai wasu hare-hare na ta’addanci da aka shirya domin ɗaukar fansa daga ‘yan ta’adda, musamman Fulani makiyaya.
Sun buƙaci gwamnatin tarayya ta inganta tsaro a jihar, ta samar da wuraren tsaro a al’umma da gudanar da cikakken bincike kan hare-haren. Sun kuma sunyi kira ga al’ummar Nijeriya da su hada kai wajen tsayawa kai da fata kan kisan gilla da tashin hankali da ake yi a ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp