Neman kirkirar sabbin jihohi da kananan hukumomi da ‘yansanda jihohi da saka sarakuna cikin sha’anin harkokin mulki da sauran su, su suka dabaibaye sauraron jin ra’ayoyin jama’a kan gyaran kundin tsarin mulki na jihohin arewa a wannan karshen mako.
Kwamitin Majalisar Wakilai na duba gyaran tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a a karshen mako a yankuna na arewa maso yammacin Nijeriya da arewa ta tsakiya da arewa maso gabas don samun shawarwari daga masu ruwa da tsaki daban-daban domin ba wa ‘yan majalisar damar yin gyare-gyare a kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
Kwamitin ya bayyana cewa ya karbi bukatu 46 na neman kirkirar sabbin jihohi, tare da bukatu 117 na kirkirar sabbin kananan hukumomi a fadin kasar nan, yana mai cewa an samu shawarwarin ne daga kungiyoyi daban-daban da ke dukkan fadin kasar nan.
Rahotoni sun bayyana cewa an yi yunkurin gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, wanda wasu lauyoyi da masu nazari suka bayyana a matsayin dabtarin da bai dace da ka’idojin dimokuradiyya ba, bayan shekaru da dama na mulkin soja.
Yunkurin ya haifar da karin kashe kudade, amma kuma ya haifar da sakamako mai kyau a baya, wanda aka kiyasta cewa, gyaran kundin tsarin mulki ya lakumi naira biliyan 20 tare da sauye-sauyen abubuwa 30 da aka yi wa kundin a cikin shekaru 20 da suka wuce.
Jagoran majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa majalisa za ta gabatar da rahoton sake duba kundin tsarin mulki wanda ake yi a halin yanzu ga majalisun jihohi 36 kafin watan Disamba na shekarar 2025.
Arewa Ta Gabas
A zaman jin ra’ayi na yanki a arewa ta Gabas, wanda aka gudanar a jihohin Borno da Gombe, kwamitin ya karbi shawarwari guda bakwai don kirkirar sabbin jihohi da kuma kirkirar kananan hukumomi fiye da 40 daga kungiyoyi daban-daban.
Masu ruwa da tsaki sun kira ga samar da Jihar Amana daga Adamawa, Jihar Sabannah daga Borno, Jihar Katagum daga Bauchi, Jihar Tangalwaja daga Gombe da Muri, Jihar Kwararafa da Jihar Sardauna ta Kudu daga Taraba.
Wani muhimmin bukatu da kungiyoyin suka gabatar sun hada da kujeru na musamman ga mata, rarraba iko da kuma gudummuwar sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya.
Shugaban taron na yankin arewa maso gabas ‘B’, Hon Isa Ali wanda ya kunshi jihohin Borno, Yobe da Adamawa, ya ce ya karbi shawarwari daga sama da kungiyoyi 50.
Haka nan, a arewa maso gabas ‘A’, a Gombe, wanda shugabanta shi ne mai tsawatarwa na majalisa, Rt.Hon. Usman Bello Kumo, ya bayyana cewa an karbi fiye da gungun shawarwari 30 daga kungiyoyi daban-daban, kungiyoyin addini da na gargajiya, da kuma mutane masu neman canje-canje ko gyare-gyare a kundin tsarin mulki.
Arewa Ta Tsakiya
A arewa ta tsakiya kuwa, fafutuka na neman kirkirar karin jihohi da hukunta gwamnonin jihohi da suka gaza ba da ‘yancin kai ga kananan hukumomi da kirkirar karin yankunan kananan hukumomi da kuma ‘yansandan jihohi sun mamaye sauraron jin ra’ayoyi jama’a.
Sauran su ne ikon jihohi na tsara dokoki da kula da bangaren hakar ma’adanai da kuma bai wa mata karin karo mai tsoka cikin harkokin gwamnati.
An gabatar da bukatun daga masu ruwa da tsaki a taron bainar jama’a na yankin ‘A’ da aka gudanar a cibiyar taro na Siyyam da ke Minna a Jihar Neja. Cibiyar ‘A’ ta kunshi jihohin Neja, Kwara da Kogi.
An ba da shawarar kirkiran jihohi da suka hada da Kainji da Edu daga Neja da Kebbi da Okura da Okun daga Jihar Kogi da Ifesuwakpo daga Jihar Kwara.
Shugaban kwamitin jagororin taron don kafa Jihar Kainji, Amb. Ahmed Musa Ibeto, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Neja, ya ce Jihar Kainji wadda ya kamata ta kunshi masarautun Borgu da Kontagora a Jihar Neja da Masarautar Zuru a Jihar Kebbi, za ta rage wuraren da ba a gudanar da su ba da yanzu haka masu fashi ke mamaye, kuma za ta taimaka wajen yaki da ta’addanci.
Arewa Maso Yamma
A lokacin taron jin ra’ayoyin jama’a na yankin arewa maso yamma yankin ‘A’ na majalisar wakilai da aka gudanar a Kaduna, masu ruwa da tsaki sun nemi a kirkiro sabbin jihohi da ‘yansandan jihohi da kuma ware kujeru na musamman ga mata a majalisa.
Wakilan daga jihohin Kano, Katsina, Jigawa, da Kaduna sun gabatar da takardun ra’ayi kan gyaran tsarin mulki, musamman ma kan rarraba iko da gwanati ga kowani bangare na kasar nan.
Taron, wanda mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Hon. Madaki Aliyu, ya jagoranci kwamitin wanda ya jawo hankulan masu ruwa da tsaki, ciki har da kungiyoyin matasa, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin addini, masana shari’a da kungiyoyin mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp