• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kirsimeti: Farashin Abinci Da Sufuri Na Tashin Gwauron Zabi

by Bello Hamza
2 years ago
in Labarai
0
Kirsimeti: Farashin Abinci Da Sufuri Na Tashin Gwauron Zabi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ana ‘yan kwanaki kadan za a gudanar da bukukuwan kiristimeti amma al’amurra na ci gaba da cunkushe wa ‘yan Nijeriya, musamman ganin hauhawar tsadar kayan abinci, tsadar harkokin rayuwa da kuma matsalar tattalin arziki gaba daya ya dakushe armashin bukukuwan kirismeti na bana.

Bincike ya nuna cewa, manyan matsalolin da suka haifar da matsalar tattalin arziki da al’ummar Nijeriya suka shiga ya hada matsalar tsaro da ta addabi sassan Nijeriya da kuma kulle iyakokin Nijeriya da gwamnati ta yi duk kuwa da an bayar da umarnin bude wasu iyakokin amma har yanzu ana dandanawa saboda tsadar kudin mota sakamakon janye tallafin man fetur da aka yi.

  • Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
  • Ashirye Muke Mu Amsa Duk Kura-kuran Da ‘Yan Jarida Suka Gano A Gwamnatinmu – Tinubu 

Iyalai da dama sun rage yadda suke cin abinci, wasu suna ci ne sau biyu ko sau daya a rana, wasu da dama kuma sun rasa yadda za su fuskanci rayuwa ganin dimbin matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta kuma ga bukukuwan kiristime ya dunfaro, babu alamar za a yi bikin cikin armashi kamar yadda aka saba a shekarun baya.

A ta bakin wani malamin jami’a mai suna Dakta Ayobami Aderemi “Bama bukatar wani mai duba don ya gaya mana cewa, iyalai da dama na cikin tsananin matsain tattalin arziki wanda shugabanin kasa suka jefa su sakamakon tsare-tsaren su na tattalin arziki, ciki har da janye tallafin man fetur da aka yi ba tare da an samar da matakai na rage radadin da al’umma za su shiga ba.

A yanzu ana sayar da buhun shinkafar waje a kan N65,000 zuwa N70,000 yayin da ake sayar da ta gida a kan N50,000.

Labarai Masu Nasaba

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Aderemi ya ce, tabbas iyalai da dama ba za su bikin kiristimeti ba a cikin walwala ba, wannan yana kara nuna alamun irin matsala da karancin abinci da za a fuskanta a Nijeriya a nan gaba.

Bincike ya nuna cewa, yawancin ‘yan Nijeriya sun yanke shawarar gudanar da bukuwan kiristime a wuraren da suke ba kamar yadda suke yi a shekarun baya ba na tafiya grurunwan su na asalin, inda za ka ga magidanci tare da iyalansa sun hau mota zuwa garuruwasu amma a wannan shekara, saboda yadda kudin mota ya yi tashin gwauron zabi sakamakon karin farashin man fetur, mutane da dama da wakilinmu ya tattauna da su sun bayyana cewa ba inda za su tafi, “Zan zauna in yi bikin a Abuja saboda yadda kudin mota zuwa kudancin kasar nan ya tashi”, in ji wani magidanci da ya bukkaci mu sakaya sunansa.

Haka kuma wasu masu sana’ar dinki sun koka a kan yadda al’umma ba su yi dinki sosai ba kamar yadda suke yi a irin wannan lokacin a shekarun baya. Hassan Tela da ke babbar kasuwar Wuse a Abuja ya ce, a irin wanna lokacin a shekarun baya har kin karbar aiki suke yi amma a wannan shekarar mutane kalilan ne suka kawo musu dinki saboda matsalar tattalin arziki da ake fuskanta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Rayuwar ‘Yan Jari-bola Bayan Fatattakar Su A Abuja

Next Post

Shirin Bunkasa Noman Alkama: Da Gaske Rijiya Ta Bayar Guga Ta Hana A Yobe?

Related

Labarai

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

5 hours ago
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

6 hours ago
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC
Labarai

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

9 hours ago
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya
Ra'ayi Riga

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

12 hours ago
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
Labarai

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

14 hours ago
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa
Labarai

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

16 hours ago
Next Post
Shirin Bunkasa Noman Alkama: Da Gaske Rijiya Ta Bayar Guga Ta Hana A Yobe?

Shirin Bunkasa Noman Alkama: Da Gaske Rijiya Ta Bayar Guga Ta Hana A Yobe?

LABARAI MASU NASABA

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.