Gwamnatin Tarayya ta sha bullo da muhimman shirye-shiryen farfado da harkokin noma, don inganta tattalin arziki, ayyukan yi tare da samar da isasshen abinci ga al’ummar kasa baki daya. Wanda a zahiri, wadannan muhimman shirye-shirye; idan an aiwatar da tsarin da yake a rubuce a takardu, hakan zai taimaka wajen kawo mafita ga wasu daga cikin wahalhalun da ‘Yan Nijeriya suke fuskanta na karancin abinci da hauhawar farashinsa.
Shirye-shiryen tallafa wa ayyukan da za su farfado da aikin noma tare da manoma sun hada da amfani da kungiyoyin manoma na kasa. Yayin da wani zubin ma’aikatar kula da aikin noma ta kasa ce ke daukar nauyin aiwatar da shirin, da zimmar ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, amma daga bisani haka al’amarin zai wuce kamar hurawar iska.
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kasafin Biliyan 437.3 Na 2024
Duka wadannan tsare-tsaren daruruwan biliyoyin naira da gwamnatin tarayya ta fitar, ba su kai banten su ba, saboda yadda suka gamu da manya-manyan kurakurai, da suka hada da rashin kwararrun mutane masu amana, da za su aiwatar da tsarin zuwa ga manufar da aka tsara shi. Saboda ta hanyar kwararru ne kadai za a bi wajen zakulo manoma na gaskiya, wanda suka dauki harkar noma sana’a, kuma dadaddu a fagen, masu kishin da za su bayar da gudunmawa wajen goya wasu kanana a bayansu don nona musu hanyar da za ta taimaki gwamnati cimma wannan burin da ta saka a gaba.
Wannan babban gibin ne ya jawo wasu maras kishi da bara-gurbin ‘yan siyasa suka yi wa shirin mummunan targaden da ya kasa kai wa zangon da aka tsara zai isa. A sa’ilin da gwamnatin tarayya ta ware wadannan makudan kudade, a matsayin tallafa wa harkokin noma, tare da kyakkyawar manufa, amma ba tare da bibiyar yadda tsare-tsaren suke gudana ba, hakan ya bai wa maras kishi kasa da ci gaban al’umma damar watanda da dukiyar yan kasa- rijiya ta bayar guga ta hana.
A wani sabon yunkurinta na tunkarar matsalar karancin abinci, hauhawar farashin kayayyakin abinci da na masarufi, samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, Gwamnatin Tarayya a karkashin shugaban kasa Bola Ahamed Tinubu, ma’aikatar kula da ayyukan noma da samar da abinci, a makon da ya gabata ta kaddamar da bai wa manoma tallafin noman alkama na rani, na bana (2023/2024) a karkashin shirin bunkasa noma na National Agricultural Growth Scheme and Agro Pocket (NAGS-AP), wanda ake sa ran noma ton 1,250,000 na alkama a kowace shekara. Kuma bisa ga kididdigar masana, idan shirin ya gudana kamar yadda aka tsara shi, zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyakin abinci, samar da aikin yi, inganta habyoyin dogaro da kai tare da habaka tattalin arziki.
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin a kauyen Kadume dake karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa, Minista a Ma’aikatar Noma ta Nijeriya, Sanata Abubakar Kyari ya ce, “A wani bangare na shirin gwamnatin tarayya wajen tallafawa kimanin manoma 150,000 zuwa 250,000 na kashi 50 cikin dari domin samun damar noma tsakanin kadada (hekta) 200,000 zuwa 250,000 wajen cimma kudurin ta na tan 1,250,000 na alkama.”
Ministan ya kara da bayyana cewa, wannan shiri na noman rani wani muhimmin bangare ne na yunkurin bunkasa noma a karkashin shirin: AgroPocket (NAGS-AP), wanda aka samar da shi ta hanyar ranto dalar Amurka miliyan 134, tare da hadi da Bankin Raya Afirka (AfDB) a Nijeriya. Ya ce babban kudurin wannan Gwamnati shi ne farfado da harkokin noman shinkafa, masara, rogo da alkama, a kasar nan.
Har Ila yau, akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta fadada adadin yawan kananan manoman zuwa sama da 42,000 tare da baiwa kowane manomi daya tallafin kayan noma kashi 50 cikin dari daga adadin kudin da gwamnatin ta kashe wanda aka kiyasta kashe naira 361,000 ga kowace kadada daya.
A hannu guda kuma, Ministan ya bai wa jami’an tsaron fararen hula (NSCDC) da sauran jami’an tsaro su sanya ido sosai wajen dakile duk wani yunkurin karkatar da kayan, sabanin yadda aka tsara aiwatar dasu.
LEADERSHIP Hausa ta jiwo ra’ayoyin wasu daga cikin manoma a jihar Yobe dangane da raba wannan tallafin noman alkama, inda kaso mai yawa suka bayyana rashin gamsuwarsu dangane da yadda gwamnatin ta raba wannan tallafin.
Alhaji Ishak Muhammad, manomi a garin Gashu’a ta karamar hukumar Bade, ya ce ba shi da masaniya kan raba wannan tallafin noman alkama, ya kada baki ya ce, “Da kimanin karfe 8:00 na dare na ga sakon kar ta kwana ya shigo wayata (ban san wanda ya bayar da lambar wayata ba) sai daga baya wani mutum (ya boye sunan shi) ya kira ni, ya ce an tura maka sakon kayan noman alkama, gobe da safe ka tafi Filin Agric Katuzu. Bayan na zo aka ce na je na nuna sakon, daga baya mutumin ya karbi kayan, ya ba ni naira 25,000.”
Wakilinmu ya gano cewa, kowane manomi zai biya naira 180,000 sannan a bashi buhu 7 na takin zamani samfurin (NPK Nagari), lita 7 na takin zamani na ruwa, tare da magungunan kashe ciyawa da kwari 4, sai buhun irin alkama (50kg) guda biyu. Sannan kimanin kaso 70 cikin dari na wadanda aka tura wa sakon karbar kayan, manoman bogi ne, yayin da wasu daga cikin su kananan yara ne da ba su zarta shekara 12 zuwa 17 ba.
Alhaji Jabbi Mai-kanwa Gashu’a, shi ne Shugaban hadaddiyar kungiyar manoma ta jihar Yobe, ya bayyana cewa, “Ni ma haka na tsinci labarin ana raba kayan tallafin noman alkama a nan jihar Yobe; babu wanda ya tuntube mu a matsayinmu na shugabannin manoma- walau Gwamnatin Tarayya ko ta jihar Yobe kan batun. Amma iya fahimtarmu, kila al’amari ne wanda yan siyasa suka yi babakere a ciki.”
“Amma idan manoman gaskiya gwamnati take nema, ya dace a tuntube mu, saboda muna cikin wannan sabga ta noma sama da shekara 70. Duk da ba mu yi mamaki ba, amma abu ne mai wahala Gwamnatin Tarayya ta cimma burinta a wannan aiki.” Ya bayyana.
Har ila yau, wakilinmu a jihar Yobe ya tuntubi daya daga cikin masu hannu wajen aiwatar da raba kayan tallafin noman alkama, Alhaji Dayyabu Gashu’a, ta wayar tafi-da-gidanka inda ya ce ba zai ce komai ba kan batun. Wannan ya haifar da alamar tambayar, da gaske rijiya ta bayar da ruwa guga ta hana?