Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bai wa Kiristoci kyautar manyan motocin shinkafa guda uku don tallafawa bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Mataimakin gwamnan na musamman kan harkokin addinin Kirista, Samuel Audu Dabai, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a Birnin Kebbi.
- Nijeriya Ba Ta Cikin Kasashe 10 Da Suka Fi Cin Bashi A Afirka – IMF
- Sin Ta Sha Alwashin Karfafa Kare Muhallin Halittun Rawayen Kogi
Dabai ya ce wannan gudunmuwar tana nuni da irin kulawar gwamnatin jihar ga al’ummar Kirista, domin tabbatar da sun gudanar da bukukuwansu cikin jin dadi da walwala.
Ya kara da cewa Kiristoci a jihar sun kammala shiri don bikin Kirsimeti, inda wasu ke komawa gida daga waje, yayin da wasu kuma ke shirye-shiryen tafiye-tafiye zuwa garuruwansu.
Dabai ya kuma sanar da cewa za a fara rabon shinkafar nan ba da jimawa ba, inda za a kai kayan zuwa yankin kudancin jihar da ke da mafi yawan mabiya addinin Kirista.