Jami’an ‘yansanda a jihar Bauchi sun kama kimanin mutane 15 da ake zargi da laifin sata, da kuma haura gidajen jama’a a ranar Kirsimeti.
An kama wadanda ake zargin ne a wani sintiri da rundunar ta gudanar domin dakile aikata laifuka a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na karshen shekara.
Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Lahadi.