Akalla otal 70 ne ke fuskantar barazanar rufewa har sai abin da hali ya yi, sakamakon rashin amfani da na’urar daukan hoto (CCTV) a Jihar Adamawa.
Wannan matakin ya biyo bayan kisan giilar da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka yi wa wata budurwa a cikin dakin wani otal a jihar.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane 29 A Kauyen Katsina
- Kotu Ta Soke Kasafin Kudin Jihar Ribas Na 2024
Farfesa Kaletapwa Farauta, mataimakiyar gwamnan jihar, ta bayyana hakan a wani taron gaggawa da kungiyar masu otal, a gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin.
Ta ce idan sun gaza sanya na’urorin CCTV, gwamnati za ta kwace lasisinsu.
Mataimakiyar gwamnan wadda ta bayyana kisan budurwar a matsayin babban abin bakin ciki, ta gargadi mambobin kungiyar masu otal a jihar da su tabbatar da tsaron lafiyar kwastomominsu a kowane lokaci.
Ta ce “Daga yanzu ba za a lamunci sakaci da rashin tsaron lafiyar jama’a a otal ba.
“Kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jiha shi ne babban aikin da gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri, ta sa a gaba” in ji Farauta.
Samuel Aduata, shi ne shugaban kungiyar masu otal a jihar, ya bai wa gwamnatin jihar tabbacin hadin kan mambobin kungiyar domin kaucewa sake faruwar irin kisan da aka yi wa budurwar a daukacin otal a jihar.
Tuni dai shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Dakta Edgar Amos, ya sanar da kafa kwamitin da zai bibiyi otal-otal domin tabbatar da ganin sun bi umarnin da gwamnatin ta kafa.