Kisan gillar babban basarake Daular Gobir, Sarkin Kudun Gatawa, Alhaji Muhammad Bawa a hannun ‘yan bindiga, ta yi matukar girgiza al’ummar jihar Sakkwato wadanda rasuwarsa a hannun ‘yan bindigar ta zo masu a- ba- zata a yayin da suke tsammamin dawowarsa a cikin iyali lafiya.
A yayin da al’ummar Sakkwato suke jimami da jajantawa kan faruwar mummunan al’amarin tare da dora alhakin hakan ga gwamnati haka ma bayanai daga masarautar Gobir da Gabashin Sakkwato ya nuna al’amurra sun tsaya cik!
- Yadda Ambaliya Ta Lalata Gidaje 255 A Garin Natsinta Da Ke Katsina
- Gwamnatin Kano Za Ta Tsara Zamantar Da Magungunan Gargajiya
Al’umma sun shiga cikin kunci da takaicin yadda basaraken wanda aka shaida da gudanar da mulkin gaskiya da adalci ya rasa ransa a hannun ‘yan bindigar duk kuwa da ikirarin da Gwamna Ahmed Aliyu ya yi a yayin yekuwar neman zabe cewa, idan duka kudin jihar Sakkwato za su kare sai gwamnatinsa ta samar da ingantaccen tsaro a Gabashin Sakkwato.
A cikin bidiyon da aka saki a karshen mako, an ga basaraken cikin yanayi na tashin hankali, sanye da tufafin da suka jike da jini kuma daure da sarkoki, yana rokon gwamnatin da ya ce ya hidimta mata tsawon shekara 45 ta taimaka masa a wannan mawuyacin hali.
Dangane da lamarin, wani dan Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato, Honarabul Aminu Boza, ya tabbatar da cewa mutumin da ke cikin bidiyon shi ne basaraken da aka sace.
Iyalin Sarkin sun nuna damuwa da takaici kan yadda suka sanar da hukuma, amma ba a sami cikakkiyar kulawa ba. Sun bayyana cewa duk da kokarin tattaunawa da masu garkuwar da suka yi, wadanda suka sace shi sun nace sai gwamnati ta shiga lamarin kafin a sako shi.
A hirarsa da BBC, Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne magajin garin na Gobir kuma daya daga cikin masu nadin sarki, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.
“Labarin da na samu shi ne ‘yan bindigar sun harbe shi ne tun a jiya Talata bayan la’asar, kuma wadanda suka je tattauna biyan kudin fansa ne suka ga gawar sarkin a kwance,” in ji shi.
Ya kara da cewa zuwa lokacin da aka yi magana da shi ba su karbi gawar mai martaban ba tukunna.
Kazalika, ya ce akwai dan sarkin mai suna Kabiru da aka yi garkuwa da su tare, kuma abin da suka saka a gaba kenan yanzu.
Magajin garin ya ce: “A ranar Talata da safe an kira shugaban masu garkuwar har ma yana tambaya game da kudin fansa. Da aka nemi a yi magana da sarkin sai ya ce yana can yana jin dumi a gefen wuta.
“Da aka yi magana da Kabiru ya tabbatar da cewa sarki na can yana jin dumi, amma ya yi ta rokon a biya kudin fansa domin kubutar da su.”
Wani dan sarkin na Gobir ya ce an yi wa mahaifin nasa kwanton-bauna ne a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa gida.
“‘Yan bindigar sun fara harbi kan mai uwa da wabi lokacin da suka hangi motar mahaifin namu, abin da kuma ya janyo fashewar tayoyin motar da karkatar da hankalin direbansa har ta kai ya tsaya,” in ji dan sarkin.
Majiyoyi daga Sabon Birni sun ce an yi garkuwa da karin mutum biyar a yankin a ranar da aka sace sarkin.