Matarsa ta ce kwana biyu na rabu da ganin abokinka Abdul a gidan nan Allah ya sa dai lafiya? Sai ya ce mun dan sami sabani da shi kwana biyu amman za mu shirya. Sai ta ce Allah sarki Abdul mutumin kirki na san yandu haka laifinka ne, kila kai ne ka bata masa rai.
Sai ya ce a’a ko kadan cewa na yi ina son sayen mota da kudin da na samu a siyasar bana shi kuma yake ba ni shawarar aure ya kamata in kara tun da na sami dama.
Na nuna kin Amincewa ta da shawararsa shi kuma ya ji haushi ya ce kwata-kwata ba na son daukar shawararsa, tun daga nan ko na kira shi a waya ba ya daukar wayata.
Sai ta ce kyle dan banza ni fa dama kaf cikin abokanka sam ban yarda da wannan mai ruwan munafukan ba.
DARASI
Rika fadar gaskiya a kan masoyi ko makiyi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp