• Leadership Hausa
Sunday, June 4, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsokaci A Kan Tsananin Kishi Ga Masoyi Ko Masoyiya

by Rabi'at Sidi Bala
12 months ago
in Taskira
0
Tsokaci A Kan Tsananin Kishi Ga Masoyi Ko Masoyiya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin tsananin Kishin da wasu ke nuna wa wanda suke so, yayin da su kuma mazan ko matan da ake so suke hangen hakan bai dace ba ko ba dai-dai ba ne a soyayya.

Musamman ta yadda idan soyayya ta yi karfi har tsananin kishin yakan zarce ya koma tamkar zargi, wanda kuma sam! ba hakan ba ne, tsananin kishin ne kawai ya saka hakan.

  • Abinci Shi Ne Tushen Rayuwa

Wasu masoyan na fuskantar barazanar rabuwa da juna ta dalilin kishin da ya tsananta ga wanda ake so. Dalilin hakan ya sa wasu daga cikin mabiya shafin TASKIRA; suka tofa albarkacin bakinsu a kan ko mene ne kishi, me yake jawo kishi, shin kishin wanda ake so yana da kyau ko babu?, Ka/kina kishin wanda ki/ka ke so, wanne irin kishi kike masa ko ka ke mata, wadanne abubuwa ne idan aka yi su, suke nuni da alamar kishi ake?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:

Sadik Ashiru daga Jihar Kano

Kishi
Kishi yana da kyau sosai ma kuwa musamman akan wanda kake so abin da ke janyo kishi ba komai bane face kauna saboda wani lokacin za ka ga mutum suna tare da budurwarsa sai a kira ta a waya ko dan uwanta haka kai kuma saurayi za ka fara tuhumarta akan wa ke kiranta a waya? ba kayi buncike ba wannan kadai ma kishi ne kuma kishi me kyau sadoda ka san wasu mutane take hurda dasu ba hakan yana da kyau sosai. Eh! ina kishin wanda nake so sosai musamman ma na ganta da wani saboda bana so maza su fiya rabarta ko da kuwa hakan da ‘yan uwanta ne ina kishinta sosai. Kwatsam! sauaryinki ya zo zan ce wajanki kawai sai ya ganki da wani a kofar gida, sannan ko kuma ita budurwarka ta kira wo ka a waya ta ji busy.

Labarai Masu Nasaba

Dabi’ar Wasu Maza Ta Kiran ‘Yan Mata A Waya A Gaban Matansu

Tsokaci Kan Maza Masu Boye Bayanan Kansu Wurin Neman Aure

Dakta Maryama ‘Yar Mutan Sakkoto:

Kishi
Shi kishi halitta ne, wanda Allah (S.W.A) ya sanya shi a cikin dukkanin zukatan bayinsa, wala’alla namiji ne ko mace. Tom mafi a kasari so, so shi ne ke kawo kishi, musamman a wurin mata, duk da cewa maza sun fi kishi sai dai su na su a boye ya ke, sabanin na mata. Zan iya cewa a wani gefen yana da kyau, haka kuma zan iya cewa a wani gefen ba shi da kyau gaba daya. Bari mu dauki gefe mai kyau, kishi mai tsafta, tsaftatacce, ba irin wanda mata su ke yi yanzu na hauka ba, kin ga wannan mai kyau ne, sa’annan shi kan shi miji ko mata muddin dayansu ya fahimci daya baya kishinsa to abin ba zai yi dadi ba. Kishi marar kyau kuwa shi ne na hauka wanda mata su ke yi yanzu, za ki ga mace akan kishi har ta je ta furta wata kalma ko ta aikata wani abu wanda zai kai ta ga aikin dana sani. Sosai kuwa, ina matukar kishin abin da na ke so, idan na ce matuka ba fa kadan ba, irin da yawa din nan. To zan iya cewa kishin da na ke yi akan abin da na ke so gaskiya mai tsafta ne. To kin ga kamar misali a karon farko inda za ki fahimci mace tana kishin mutum alal misali saurayi, tashin farko idan ta ji sunan wata a bakinsa, nan da nan fuskarta da ma yanayinta zai canja. Ko yanzu lokacin ‘status’ din nan, za ki ga saurayi ya daura hoton budurwa ko bashi da alaka da ita ya sanya ML da alamar heart din nan, to a lokacin da budurwar ta duba ‘status’ din kar ki so ganin yadda yanayinta zai canja. Note! Bana fadi haka bane dan maza ku samu abin gasa mana zukata ba, misali ne nayi, dan ba lallai ba ne idan ku ka yi haka mu ji wani abu ba loz!

Zara Muhammad Sunusi (Ummu Heebbat) Gaidam Jihar Yobe:

Kishi
A nawa tunanin kishi shi ne; Nuna damuwa akan abin da kake so wajen bashi kulawa sosai yadda zuciyar sa za ta tsaya a gare ni. Abin da yake jawo kishi shi ne; Ganin abin da kake kauna yana karkata hankalinsa wani guri daban ba kai ba musamman idan kasan cewa kana iya kokarinka wajen bashi kulawa. Tabbas! kishi akan abin da kake so yana da kyau. Saboda dukkan mutumin da ba shida kishi akan matarsa Annabi ya ce dayyus ne haka zalika a gurin mace ya kamata a ce ta zama mai kishi a gun mijinta amma kishi irin na addini. Sosai ina kishi akan wanda nake so, ina masa kishi ne irin na addinin musulunci sannan ina kishinsa idan na ga ya yi kwalliya sosai zai fita. Abin da masoya suke yi wanda ake gane cewa kishi ne sune; Idan ka ga mace tana fushi yayin da ta ga kana kasa da murya shi ma kishi ne, ko ta ga kayi kwalliya kana saurin fita za ka ga tayi kici-kici da rai shi ma kishi ne, ko kuma ka ga tana shareka akan ta ji wayar ka ‘busy’ shi ma kishi ne.

Ummu Maher (Miss Green) Jihar Kano:

Kishi
Kishi halitta ne da Allah ya ke yi mana musamman mu mata, kishi halal ne mace ta yi sa musamman a kan mijinta, don kishi hatta annabawa ma sun yi shi, sai dai an fison mace ta yi kishi na sunna ba kishin hauka, hatta ubangijinmu yana da kishi don haka ma bai san a hada shi da ko wani abu a duniya. Gaskiya ina da kishi akan wanda na ke so musamman miji na, kuma ina kishinsa amman kishin da na ke yi mai bai saba da sunnar ma’aiki ba. Ta yadda za a gane akwai kishi jin haushi idan ka ga wanda ka ke so yana kula wata, jin haushi idan wata mace ta yi wa wanda ka ke so magana.

Fatima Batula Jihar Kaduna:

Kishi
Kishi wani halitta ce da Allah ya yi shi a zukatan bayinshi. Tarayya akan wani abu da kake so. Sosai ma dan ko ubangijin mu yana da kishi, yana da kyau kishin abin da ake so. Hhhh kwarai da gaske kuwa ina kishin mijina, kishi dai bayan ‘yan uwa da abokanan hulda bana so yana kallo ko magana da wata bayan ni, jin haushi idan yayi /tayi magana da wani / wata, jin haushi idan yana/tana yawan ambaton wani/wata.

Hannah Mahmoud Suhana (Hajiya Duduwa Me kan Bari) Birnin Yero Jihar Kaduna:

Kishi
A nawa tunanin kishi shi ne nuna damuwa akan abun da kake so a takaice, abin da yake jawo kishi kuma abubuwa ne da yawa amma babba a cikin su shi ne kaiwa matuka wajen so da kaunar abun da kake so, na’am (eh) yin kishi akan wanda kake so yana da kyau sai dai kishin ayi mai tsafta ma’ana a yi shi bisa tsari. Na’am (eh) ina kishi akan wanda nake so, hmmmm to a gaskiya ina yi masa kishi ne irin wanda shari’ar musulunci yace ayi da kuma na al’ada misali ina kishinsa idan naga yana aikata sabon Allah akan ya daina saboda ban so ya fuskanci azabtarwar Ubangiji, Kishi idan ka ga abin sonka da wasu, Kishi idan ka ga abin sonka yana damuwa da wasu fiye da kai, Kishi idan ka ga abin sonka ya fi karkata wani gefe fiye da kai.

Hafsatu Yusuf Daga Jihar Kano Unguwar Gadon Kaya:

Kishi
A tunani na kishi wani abu ne wanda tun daga farko ya samo asali wajensu Nana Aisha da kuma Nana Khadija gashi ya zo har zuwa kanmu kuma dole idan kana san abu dole kayi kishinsa sabida kaunar da kake yi masa idan ba ka kishin abin da kake so toh wallahi ba kaunarsa kake yi ba kishi ya zama dole a tare damu. Ina kishi akan wanda nake so sosai sabida ina kaunarsa feye da yadda baya zato shi ma kuma na san yana kaunata dole nayi kishinsa babna so nabga ya kula wata zuciyata ba ta dadi sabida ina kyautata masa nima kuma yana kyautatamin, baya so na kula wani in ba shi ba, ba na so ya kula wata in ba ni ba, ba na so yayi zaman majalisa.

Zahra’u Abubakar (Dr Zara):

Kishi
Kishi shi ne ka ji idan wani ko wata ya rabi abun kaunar ka ka ji ba dadi ko kuma ranka ya baci, kauna da soyayya ce take kawo kishi, kishi akan wanda kake so yana da kyau matuka. Ina kishi gaskiya akan wanda nake so, ko irin ace ka canza hotan dp dinka, ko ace da wa kake? waya? ga sunan dai da da yawa.

ShareTweetSendShare
Previous Post

A Kullum Cikin Damuwa, Bacin Rai Da Bakin Ciki Nake Kwana Kan Matsalar Tsaro —Buhari

Next Post

Sin Ta Gudanar Da Ayyukan Nazarin Kayan Tarihi Fiye Da 8800 A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

Related

Dabi’ar Wasu Maza Ta Kiran ‘Yan Mata A Waya A Gaban Matansu
Taskira

Dabi’ar Wasu Maza Ta Kiran ‘Yan Mata A Waya A Gaban Matansu

2 weeks ago
Tsokaci Kan Maza Masu Boye Bayanan Kansu Wurin Neman Aure
Taskira

Tsokaci Kan Maza Masu Boye Bayanan Kansu Wurin Neman Aure

3 weeks ago
Tsakanin Mace Mai Bala’in Son Kudi Da Mai Yawo, Da Namiji Mai Kulle Ko Mako, Wanne Ne Dama-dama?
Taskira

Tsakanin Mace Mai Bala’in Son Kudi Da Mai Yawo, Da Namiji Mai Kulle Ko Mako, Wanne Ne Dama-dama?

4 weeks ago
Dubi Ga Batun Cewa, ‘Ba A Yin Budurwa Ranar Sallah’
Taskira

Dubi Ga Batun Cewa, ‘Ba A Yin Budurwa Ranar Sallah’

1 month ago
Tsokaci A Kan Sabanin Da Ake Samu Wurin Mu’amala
Taskira

Tsokaci A Kan Sabanin Da Ake Samu Wurin Mu’amala

3 months ago
Yadda Za Ki Zauna Tare Da Surukai Masu Sa Ido
Taskira

Yadda Za Ki Zauna Tare Da Surukai Masu Sa Ido

3 months ago
Next Post
Sin Ta Gudanar Da Ayyukan Nazarin Kayan Tarihi Fiye Da 8800 A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

Sin Ta Gudanar Da Ayyukan Nazarin Kayan Tarihi Fiye Da 8800 A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

LABARAI MASU NASABA

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

June 4, 2023
Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

June 3, 2023
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Tsarin Wayewar Kan Kasar Sin Mai Dacewa Da Zamani

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Tsarin Wayewar Kan Kasar Sin Mai Dacewa Da Zamani

June 3, 2023
Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Wuraren Al’adun Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Wuraren Al’adun Sin Tana Da Babbar Ma’ana

June 3, 2023
Sin Ta Jaddada Kira Ga Sassan Masu Ruwa Da Tsaki A Rikicin Sudan Da Su Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta

Sin Ta Jaddada Kira Ga Sassan Masu Ruwa Da Tsaki A Rikicin Sudan Da Su Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta

June 3, 2023
Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari

Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari

June 3, 2023
‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Yahaya Bello Hari, Sun Raunata Jami’an Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Yahaya Bello Hari, Sun Raunata Jami’an Tsaro

June 3, 2023
Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

June 3, 2023
Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Mauricio Po-chettino?

Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Mauricio Po-chettino?

June 3, 2023
Sin Ta Yi Tir Da Kalaman Sakataren Tsaron Amurka A Taron Shangri-La

Sin Ta Yi Tir Da Kalaman Sakataren Tsaron Amurka A Taron Shangri-La

June 3, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.