Tuni masu fashin baki kan al’umaran da ke wakana a fagen siyasar Nijeriya suka zuba hajar mujiya da kasa kunne domin ganin ko auren takarar da ake neman kullawa a tsakanin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da takwararsa na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi dai dauru ko dai za a hakura tun kafin gemu da gemu su hadu.
Shi dai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kara karfafa yiwuwar kulla kawance da takwararsa Mista Peter Obi ne domin su kara samun karfin fuskantar babban zaben shekarar 2023.
A wani bayani da ya yi wa gidan Rediyon BBC kwanan nan, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa, “Tabbas muna tattaaunawa da bangaren Peter Obi, tuni muka kafa kwamitin da ke tattaunawa don fitar da hanyoyin da za mu kasance tare da fito da yadda za mu fuskanci lamarin, abokananmu da masu yi mana fatan alhairi sun dukufa don ganin mun hade, saboda sun yi amanna akwai alhairi tattare da hakan.”
Tsohon gwamnan ya kuma kara da cewa, hadewarsu na da matukar muhimmanci musamman ganin yadda jam’iyyun APC da PDP ba su yi lissafin da ya kamata ba musamman idan aka dubi yankin Kudu maso Gabas, “hakan zai ba mu magoya baya daga yankin Ibo, in aka lura kuma da farin jinin Peter Obi a yankin na Ibo gashi kuma ya samu karbuwa a sassan kasar nan, hakan zai taimaka mana samun nasarar lashe zabe ba tare da wahala ba” in ji shi.
Idan za a iya tunawa, Peter Obi ya sauya sheka ne daga jam’iyyar PDP tun kafin a kai ga zaben fid da da gwanin da ya bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubukar damar zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Ya danganta shawarar tasa ce a kan yadda abubuwa suka sukurkuce a jam’iyyar adawar, daga nan ne ya koma jam’iyyar LP inda suka tsayar da shi takarar shugabancin kasa.
A nasa tsokacin, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi, Mista Okupe, a tattaunawar da ya yi da wani gidan radiyo mai zaman kansa a Legas a karshen mako, ya ce, babban burinsu a nan shi ne lashe zaben shugaban kasa, kuma za su yi duk abin da ya kamata na ganin sun cimma burinsu, wanda hakan ne kuma burin mafi yawan matasan Nijeriya.
“Muna bincike don dauko wanda bai kai Obi a shekaru ba don ya zama mataimakinsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2023”, in ji shi.
Tsohon hadimi ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan ya tabbatar da cewa, za su zabi dan takara shugabancin kasar ne a matsayin na wucin gadi a daidai lokacin da suke tattauna yiwuwar kulla kawance a zaben 2023.
Ya kuma ce, kasancewa matasan Nijeriya sun rungumi akidun jam’iyyar Labour Party, kuma a shirye suke su bayar da gudummawarsu don a samu nasarar kai kasarmu tudun mun tsira, “sun yi amanna da shugabancin Peter Obi, a kan haka na yarda cewa, za su amince da hadewa da NNPP don mu cimma burinmu na kafa mulki a Nijeriya. A shirye muke mu bayar da dukkan gudummawar da ake bukata wajen samun nasarar wannan hadakar da muka sa a gaba.”
A wani bangaren kuma, jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP mai alamar kayan marmari, ta tabbatar da cewa, tattaunawarta da jam’iyyar Labour Party (LP) na duba yiwuwar hadewa na nan daram tana kuma tafiya yadda ya kamata.
Jam’iyyar ta ce, dan takararta na shugaban kasa Sanata Dakta Rabiu Kwankwaso, zai iya karbar mukamin mataimakin shugaban kasa ga dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi in har hakan zai zama maslahar da ake bukata.
Akwai dai rade-radin da ke nuna cewa, ‘yan takarar biyu na iya hadewa don samar da wata hadakar da za ta iya fafatawa tare da samun nasara a kan manyan jam’iyyun kasar nan Peoples Democratic Party, PDP, da All Progressibes Congress, APC wanda ake ganin al’ummar Nijeriya sun gaji da salon mulkinsu.
Da aka tambaye shi yadda hadakar za ta kasance, Sakataren watsa labarai na jam’iyyar NNPP, Dakta Agbo Major, ya bayyana wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa, a halin yanzu ana cigaba da tattaunawa a kan haka, kuma ba zai yiwu a riga malam masallaci ba, amma daya daga cikinsu zai amince da zama dan takara, daya kuma mataimakinsa.
“Yayin da muka kammala tattaunawar, ‘yan Nijeriya za su yi murna da abin da muka cimma,” in ji shi.
Tuni dai fostar yakin neman zabe dauke da hoton tsohon gwamnan na Ananmbara Peter Obi da tsohon gwamna Jihar Kano Rabiu Kwankwaso a matsayin mataimakinsa a zaben 2023, suka karkade manyan garuruwan tarayyar Nijeriya.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto dai ba a kai ga matsaya a kan a wace jam’iyyar ce za su shiga takarar ba, sai da ana raderaden cewa a jam’iyyar Kwankwaso ta New Nigerian People’s Party, NNPP ma alamar kayan marmari ce za a yi amfani da ita wajen takarar hadakar.
Masu fashi bakin harkokin siyasa sun bayyana cewa, wanna hadakar za ta iya bayar da mamaki a zaben 2023, musamman ganin cewa a halin yanzun Jam’iyyar NNPP tana samun karbuwa kwarai da gaske a yanki Arewacin Nijeriya, cikin manyan ‘yan siyasan da suka rungumi jam’iyyar a ‘yan kwanakin nan sun hada da tsohon Ministan wasanni Solomon Dalung, da daya daga cikin tsohon na hannun daman Shugaba Buhari, Buba Galadima.
A bin tambaya a nan shi ne, shin wannan hadakar za ta yiwu kuwa? Kuma wane alfanu ko rashin alfanu za ta haifar, shin za ta iya taka wa manyan jam’iyyun nan na APC da PDP burki a hankoron su na lashe zaben 2023?
Wadannan tambayoyi da sauransu ke cike a bakin al’ummar Nijeriya da dama.
Da yake tsokaci kan haka, wani mai sharhin siyasa a Nijeriya Malam Muhammad Bashir ya bayyana cewa wannan kawance zai yi wahalar kulluwa, domin “idan aka duba, tsakanin Kwankwaso da Obi sarakai ne guda biyu, waye a cikinsu zai yarda ya zama Galadima? Wannan shi ne babban kalubalen da suke fuskanta, amma da za su fahimci juna a samu cikin sauki daya ya yarda ya zama mataimaki kawancen za ta ba su damar gigita tunanin APC da PDP.” In ji shi.
A yanzu dai za a iya cewa lokaci ne kawai zai bayyana yadda al’amarin zai kasance, don kuwa masu iya magana na cewa, ba a sanin maci tuwa har sai miya ta kare.