A daren ranar Lahadi Barcelona ta buga wasa mafi kayatarwa a wannan kakar wasanni ta bana bayan ta doke abokiyar karawarta Athletico Madrid duk da cewar Athletico din ta jefa kwallaye biyu a ragar Barcelona a minti 70 na wasan.
A kokarin da take yi na sake darewa kan teburin Laliga, Barcelona ta zura kwallaye 4 a cikin minti 20 domin komawa gida da maki uku, Lewondowski, Ferran Torres da Lamine Yamal ne su ka jefawa Barcelona kwallayenta.
- Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya
- Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu
Julian Alvarez na Athletico Madrid ya fara bude kasuwa a Wanda Metropolitano tun kafin zuwa hutun rabin lokaci, Alexander Sorloth ne ya kara ta biyu a minti na 70 da fara wasa lokacin da Conor Gallagher ya bashi kwallo cikin yadi na 18.
Barcelona na matsayi na daya da maki 60, inda suke da maki daya da Real Madrid dake matsayi na biyu, amma kuma Barcelona na da wasa daya a hannu wanda basu buga ba sakamakon mutuwar babban likitan kungiyar, Atletico ta ci gaba da zama a matsayi na uku akan teburin gasar Laliga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp