Hukumar tace fina finai da dab’i ta jahar Kano ta bayyana cewa biyo bayan korafe-korafen da al’umma ke yi a kan shirya fina-finan da ke nuna fadan Daba da harkar Daudu a jihar Kano, shugaban Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano Abba El-mustapha ya ba da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan da ke nuna fadan Daba da harkar Daudu a fadin jihar Kano.
Abba El-mustapha ya bayar da wannan umarni jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da manyan ma’aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano tare da wasu daga cikin wakilan ‘yan masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood wanda suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS DIRECTORS da kuma PRODUCERS.
- ‘Yan Ta’adda Sun Yi Yunƙurin Ƙwace Iko Da Sakatariyar Jihar Oyo
- Cinikayyar Shige Da Fice Ta Sin Ta Daga Da Kaso 5% A Rubu’in Farko Na Bana
Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin ya ci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar da ke jihar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su ci gaba da yaduwa a cikin al’umma.
Abba El-mustapha ya gode wa yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood dangane da hadin Kai da kuma goyan bayan da suke baiwa Hukumar a koda yaushe, daga karshe ya kara gode wa al’ummar jjhar Kano kan irin hadin kan da suke bawa Hukumar musamman na sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saba da al’ada tare da tarbiyar addinin musulunci.
Abba El-mustapha ya kuma yi alkawarin ci gaba da barin kofar sa a bude domin karbar shawarwari ga duk wadanda suke da bukatar hakan.
A ‘yan kwanakin nan wasu unguwanni da ke Kano suna fama da matsalar karuwar masu aikin daba da sauran miyagun ayyuka,wadanda wasu suka alakanta hakan da yawan kale-kallen fina finan Hausa da ake nuna yadda ake yin daba da fashi da makami da matasa keyi a halin yanzu.
Hakan yasa hukumar tace fina finai da dab’i ta jahar Kano karkashin jagorancin shugabanta Abba El Mustapha ta bayyana matakin dakatar da nuna duk wani shiri dake nuna aikin daba a fadin jahar ta Kano mai tarin al’umma fiye da mutum miliyan 15.