ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Ina Cikin Gwamnatin Tinubu, Zan Faɗa Wa APC Gaskiya – El-Rufai

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
Gwamnati

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana a yau Alhamis cewa, ko da yana cikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ra’ayinsa game da yadda ake tafiyar da mulki ba zai canza ba.

El-Rufai ya mayar da martani ne ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, wanda ya soki kalaman El-Rufai na cewa ƙasar na fuskantar “ gaggawa” a fannin mulki da ƴan adawa.

  • Fashewar Tayar Jirgi A Kano: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Max Air Na Tsawon Watanni Uku
  • Rundunar Ƴansandan Kano Ta Kori Wani Jami’i Saboda Karɓar Na Goro

A taron da aka yi a Abuja kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya, El-Rufai ya caccaki APC da yadda babu cikakken tsari a jam’iyyar, yana mai cewa, “Ban gane jam’iyyar APC ba, babu wani taron jam’iyya da aka yi cikin shekaru biyu – babu majalisar koli, babu NEC, babu komai. Babu ma wanda ke tafiyar da jam’iyyar; ba mutum ɗaya bane, babu kowa ma.”

ADVERTISEMENT

Bayan wannan, jam’iyyar APC ta maida martani, tana zargin El-Rufai da cin amana da ƙoƙarin ɓata wa jam’iyya suna. Wannan ya sa Bwala ya tambaye shi a shafinsa na X cewa, “Da kana cikin gwamnati, da har yanzu za ka riƙe wannan matsayi?”

A martaninsa, El-Rufai ya bayyana cewa tun farko bai taba buƙatar muƙami a gwamnatin Tinubu ba, yana mai cewa, “Na riga na zama minista shekaru 22 da suka wuce, kuma na shaida wa Asiwaju tun farko cewa ba na buƙatar wani muƙami a gwamnatinsa.”

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Ya ƙara da cewa, “Da har yanzu ina cikin wannan gwamnati, zan fadi gaskiya a cikin tarurruka na sirri, kuma idan ba a ɗauki mataki ba, zan yi magana a fili. Duk wanda ke shakkar haka, ya duba tarihin aikin gwamnati na tun daga 1998.”

El-Rufai ya kuma soki wasu da ya kira “’yan amshin shata” a gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna amfani da kuɗaɗen tsaro don kare duk wani abu da gwamnati ke yi, ko da kuwa ba abin karewa bane. Ya buƙaci Bwala da ya tuna cewa “Alkawari na farko shi ne ga Allah da ƙasa, kafin wani mutum ko hukuma.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Next Post
Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamna Lawal ya Yaba Wa DSS Kan Bankaɗo Makamai A Jihar Zamfara 

Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamna Lawal ya Yaba Wa DSS Kan Bankaɗo Makamai A Jihar Zamfara 

LABARAI MASU NASABA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.