Har yanzu tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles na da damar samun gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026, duk da cewa dai damar ba mai yawa ba ce kuma za ta dogara ne da sakamakon wasu wasannin da hukunce-hukuncen da suke gaban FIFA na wasu wasannin.
Nijeriya ta shiga cikin rashin tabbas ne bayan canjaras 1-1 da ta je ta buga da tawagar Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a yammacin Talatar satin da ya gabata wanda wannan wasan shi ne ya sake nisanta Nijeriya da zuwa gasar cin kofin duniya
Sakamakon ya sa Afirka ta Kudu ta ci gaba da zama a mataki na 1 da maki 17 cikin wasanni takwas a Rukunin C, yayin da Benin ke biye mata da maki 14 sai kuma Nijeriya da ƙasar Rwanda kowace tana da maki 11 a mataki na uku da na huɗu.
Lesotho na da maki 6 a mataki na 5, sai kuma Zimbabwe ta ƙarshe da maki 4.
Tawaga tara ko 10 ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar kofin duniya da ƙasashe 48 za su fafata, wadda ƙasashen Amurka da Meɗico da Canada za su karɓi baƙunci.
Duk tawagar da ta ƙare a mataki na ɗaya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka, ita ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zaɓo huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na 2, inda za a fitar da ɗaya daga cikinsu sannan ta kara da takwararta ta wata nahiyar.
Rabon da Nijeriya ta samu gurbin Kofin Duniya tun a 2018 da aka yi a Rasha, inda ta gaza zuwa na 2022 a Ƙatar wanda tawagar ƴ anwasan ƙasar Argentina ta lashe ƙarƙashin jagorancin Lionel Messi. Jimilla Nijeriya ta je gasar Kofin Duniya sau shida a tarihi – 1994, 1998, 2002, 2010, 2014, 2018.
A wasannin neman gurbin na gasar 2026, wasanni biyu kacal Nijeriya ta ci
cikin wasa takwas, ta yi canjaras biyar da rashin nasara ɗaya. A lissafi, Nijeriya za ta iya samun gurbi saboda wasa biyu-biyu suka rage wa tawagogin, inda take da damar samun ƙarin maki shida daga cikinsu idan ta doke Lesotho da Benin a watan Oktoba mai zuwa.
Amma yanzu abin tambayar shi ne ko tawagar ta Super Eagles za ta iya doke su ƙasashen Banin da Lesotho? Idan ta doke su, shin hakan zai sa ta samu gurbin zuwa gasar?
Duk da cewa Nijeriya ta fi ƙarfin Benin da Lesotho a fagen ƙwallon ƙafa, babu tabbas game da nasararta a kansu, saboda wasan farko da Nijeriya ta buga da tawagogin biyu 1-1 suka tashi da kowaccensu.
Wajibi ne Nijeriya ta ci wasannin biyu, abin da zai sa ta haɗa maki 17 kamar na Afirka ta Kudu, sannan kuma ta yi fatan a doke Afirka ta Kudun a wasa biyun da za ta buga da Zimbabwe da kuma Rwanda.
Ko da Nijeriya ta yi nasara a wasa biyun kuma an cinye Afirka ta Kudu, dole ne sai Super Eagles ɗin ta ci ƙwallaye fiye da shida domin ta wuce Afirka ta Kudun a yawan ƙwallaye.
Yanzu haka Afirka ta Kudu na da yawan ƙwallaye +8, yayin da Nijeriya ke da +2. A gefe guda kuma, Rwanda ma na iya kawo wa ƙasashen biyu cikas idan har ta samu irin nasarar da Nijeriya ke buƙata, amma ita tana buƙatar ƙwallaye aƙalla 9 domin ta kamo yawan na Afirka ta Kudu.
Amma duk ba ma wannan ba a cikin wannan satin ne kotun da ke karɓar ƙorafe-ƙorafen harkokin wasanni ta duniya ta yanke hukuncin kwashe maki shida a hannun ƙasar Eƙuatorial Guinea, bayan da aka samu ƙasar da laifin saka ɗan wasan da bai cancanta ya buga mata wasa ba, wato Emilio Nsue,
Eƙuatorial Guinea dai ta yi amfani da ɗan wasan ne a wasannin da ta samu nasara a kan ƙasashen Namibia da Liberia, kuma ɗan wasan suka saka shi ne ya zura ƙwallayen da suka samu nasara.
A watan Mayu ne dai hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya FIFA ta yanke hukuncin ƙwace maki shida a hannun ƙasar Eƙuatorial Guinea, sai dai ƙasar ta ɗaukaka ƙara zuwa kotu kuma kotun ta tabbatar da hukuncin FIFA.
FIFA dai ta ce ɗan wasan ba shi da lasisin bugawa Eƙuatorial Guinea wasanni duk da cewa ya shafe kusan shekaru 10 yana bugawa ƙasar wasa, amma kafin nan ya taɓa bugawa tawagar matasa ta ƙasar Spaniya wasa kuma bai samu takardar canja ƙasa ba daga hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya.
Bayan da kotun wasanni ta yi fatali da ɗaukaka ƙarar da Eƙuatorial Guinea ta yi, hukuncin ya shafi rukunin sosai ciki sannan ya shafi yiwuwar ko Nijeriya za ta iya samun damar zuwa gasar ta duniya.
Hukuncin ya matsar da Eƙuatorial Guinea daga mataki na biyu da maki 16, inda yanzu ƙasar ta dawo mai maki 10 kuma ya sa ƙasar Namibia ta koma mataki na biyu da maki 15.
Bugu da ƙari, hukuncin ya sa yanzu Nijeriya ta fara jin ƙanshin zuwa gasar amma za ta iya zuwa ne a matsayin wadda ta yi ta biyu mai mai da yawa, wanda ake kira (second best) da turanci.
A cikin ƙasashen da suke mataki na biyu a rukunansu, ƙasar Gabon ce a gaba domin tana da maki 19, sai Madagascar da Jamhuriyar Dimokraɗiyar Congo masu maki 16 kowacce, sai ƙasar Burkina Faso da Namibia da Uganda, duka suna da maki 15, Benin tana cikin rukunin Nijeriya da maki 14, hakan yana nufin Nijeriya tana buƙatar kasancewa a cikin waɗannan ƙasashe domin samun tikitin.
Wani ƙarin ƙwarin gwiwar da Nijeriya take da shi shi ne, ƙasar Afirka ta Kudu ma za ta iya fuskantar kwashe mata maki idan har FIFA ta tabbatar ƙasar ta saka ɗan wasa Teboho Mokoena, wanda bai kamata ya buga mata wasa da Lethoso ba saboda ya samu katin gargaɗi guda biyu, amma duk da haka Afirka ta Kudu ta yi amfani da shi a fafatawar.
Idan har hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya ta samu Afirka ta Kudu da laifin, babu shakka za a ƙwace makin da ta samu a kan ƙasar Lethoso, wanda hakan zai sa Afirka ta Kudu ta dawo mai maki 14 maimakon 17, iri ɗaya da Benin kenan.
Hukuncin zai dagula lissafin rukuni na C, a yayin da Nijeriya ke shirin buga ragowar wasanni biyun da suka rage mata da ƙasashen Lethoso a can ƙasar da kuma wanda za a buga a nan gida Nijeriya da ƙasar Benin a wasan ƙarshe. Idan har Nijeriya ta iya samun maki shida a waɗannan wasannin sannan aka kwashe maki 3 a wajen Afirka ta Kudu tabbas Nijeriya za ta iya samun tikitin gasar.
Ƙasashe 9 ne daga nahiyar Afirka za su samu tikitin gasar kai tsaye, sai kuma ƙasashe huɗu da suka fi samun maki (second best) za su buga wasannin share fage a samu cikon ƙasa ɗaya da za ta cike ƙasashe 10 daga Afirka.
Kawo yanzu Nijeriya tana fatan irin hukuncin da aka yi wa Eƙuatorial Guinea ya faru a kan Afirka ta Kudu a nan gaba kaɗan, wanda hakan zai sake buɗe wa Super Eagles damar samun tikiti. Ƙasashen Amurka da Canada da Meɗico ne dai za su karɓi baƙuncin ƙasar cin kofin duniya da za a buga a shekara mai zuwa ta 2026.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp