Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.
A yau shafin namu yana ci gaba da bayani ne kan abin da ke kawo warin gaba:
Auduga mai laushi na taimakawa wurin bai wa gaba iska kuma yana yin kyakkyawan aiki a wurin kawar da gumi da ruwa daga jikinku. Yawan danshi zai iya sa ki kamu da kwayoyin cuta da za su yi wa gabanki illa.
Sannan ya kamata ki kula da yawan sauya kamfai da siket saboda idan suka yi datti kuma kika maimaita su to akwai yiwuwar su haifar da warin gaba.
Sanin lokacin ganin likita:
Idan wannan warin yana tare da alamun da ba ku saba gani ko ji ba, ya kamata ku guji yin magani a gida ku tuntubi likitoci.
Misali: Idan warin gaba ya fi na al’ada karfi kuma kin lura cewa yana kara karfi, to kina bukatar ganin likita.
Haka nan, idan kin ji gabanki ya fara wari kamar na “kifi” wannan ma ya kamata ki yi saurin ganin likita. Wari mara kyau alama ce ta kamuwa da cutar gaba. Ba za ku so ku jinkirta magance matsalar ba domin cutar gaban da ba a nemi maganinta ba kan iya jawo matsalar rashin haihuwa idan ta dade ana fama da ita.
Wasu ruwa da ke fitowa daga gaban mace na iya zama na ka’ida. Idan kin lura da canji a launin ruwan, misali launin da kika saba gani fari ne ko bai da kala amma sai kika fara ganin wani launin daban, to zai iya yiwuwa kin kamu da cuta.
Yawanci kaikayin al’aura ba matsala ba ce, amma idan kuka fara jin kaikayin ya fara yawa ko kuma ya fara zafi da radadi, to alama ce na babbar matsala.
Hanyar magance sake warin gaba:
Da zarar kin kawar da warin gaba wanda ba a saba ji ba, to ki kiyaye wadannan shawarwari don hana wata matsalar.
Kula da cin lafiyayyen abinci mai sinadiran gina jiki. Yawaita cin ‘ya’yan itace, da kayan lambu. Daidaitaccen abinci yana samar da lafiyayyen jiki, kuma hakan ya hada da gabanki.Kasance mai yawan shan ruwa. Shan ruwa mai yawa yana da amfani sosai a dukkan jiki ba sai ga fata ba kawai. Yana iya taimaka wa ga lafiyar gabanki, kuma ta hanyar karfafa gumi mai kyau.
Ki dinga wanke gabanki kafin saduwa da kuma bayan saduwa. Jima’i kan iya kawo yaduwar kwayoyin cuta da maniyyi daga kwaroron roba.
Ku daina amfani da matsattsun kaya. Tufafi masu matsewa ba sa barin gabanku ya sha iska. Samun isasshiyar iskar na da muhimmanci ga lafiyar gaban mace.