• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kin San… Sirrikan Nuna Soyayya Ga Miji?

by Sulaiman, CGTN Hausa and Bilkisu Tijjani
1 year ago
Soyayya

Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.

A yau shafin na mu zai yi magana ne akan yadda wasu mata suka dauki kansu da cewa wai su sun girmi yin soyayya.

Wai sun girma ba a soyayya:

Yanzu dai bari na fara da ke uwargida; Ya kamata ki saurari duk nasihohin da zan miki, ki gode wa Allah wurin yin amfani da baiwar da ya yi miki, na kasancewa uwargida, wato komai dai yana hannunki ne har da shi kansa maigidan naki, a daidai wannan gabar in ka ji mace tana kukan yadda sitiyarin maigidan ya yi karfi, har ta kai ga cewa ba ta iya juyawa, to ta binciki kanta.

LABARAI MASU NASABA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

Hakika Allah S.W.T yana cewa:

“An kawata wa mutane son ababan sha’awa daga mata”.

Asali ke abar sha’awa ce ko kin yi ado ko ba ki yi ba, to me zai sa ba za ki yi adon domin ki karkato da hankalin maigidanki zuwa gare ki ba. Wasu matan su kan kalli wasan kwaikwayon Indiya sai su rika sha’awar yadda maza suke ma’amalla da matansu, wasu kuma wasu kuma wasan kwaikwayon Hausa suke kallo, to amma akwai wani abin lura, shi ne, shin mu a wannan matattarar tamu, mace ta kan kure adaka ta sha turare ga lalle yana daukar hankali, ta saka kayan da za su rika fizgar hankalin mai kallo don kawai ta yi rawa a gaban maigidanta ta tayar masa da sha’awarsa ya ji yana bukatarta.

Mai yuwuwa wani ya ce wannan al’adar Yahudu da Nasara ce, ko ita matar malam Bahaushe ta ce haba wannan ai sai yara mu mun girma ko ta ce sai kuma a ganki tsofai-tsofai da ke ga yara sun isa aure kina yi wa maigida rawa to amma kuma tana bukatar soyayyarsa.

Asshaikh Nasiruddeen Al’Albani RH ya fitar da wata fatawa a cikin majallar (Mujallatul Asaalah 8/ 74) yake cewa rawar da mace za ta yi a gaban maigidanta rawa kawai da aka saba ba wai na gaban jama’a ba (ba wai a wasan kwaikwayo da wuraren bukukuwa ba), kuma ba koyo ta yi masamman don ta rika yi ana gani ba, wannan ko da za ta motsa sha’awar maigida babu wani nassi da ya haramta, amma da sharadin cewa daga ita sai maigidanta kawai.

An tambayi malam cewa: To in ta saka irin kayan da masu rawa a wasannin kwaikwayo suke sakawa tsaya a gaban mijinta, ashe wannan ba koyi da su take yi ba, kuma da nuna kauna ga abin da suke yi, sai ya ce “Wannan halas ne matukar a tsakankanin ma’auratan ne, kuma ba wani ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)
Uwargida Sarautar Mata

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

October 12, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?
Uwargida Sarautar Mata

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

September 12, 2025
aure
Uwargida Sarautar Mata

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
Next Post
Ambaliya: Gwamna Dauda Lawal Ya Nuna Alhini Da Mika Jaje Ga Al’ummar Gummi

Ambaliya: Gwamna Dauda Lawal Ya Nuna Alhini Da Mika Jaje Ga Al'ummar Gummi

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 

October 14, 2025
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa 

October 14, 2025
Kotu

Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta

October 14, 2025
Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin

October 14, 2025
Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya

October 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo

October 14, 2025
Asuu

An Janye Wajibcin Samun Kiredit A Darasin Lissafi Ga Ɗaliban Fannin Zamantakewa Don Shiga Manyan Makarantu 

October 14, 2025
Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.