Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana kashe Naira miliyan ₦150m kowane wata don kula da tsaftar jihar. Da yake jawabi a yayin ƙaddamar da aikin kwashe sharar manyan magudanan ruwa a shekarar 2024 a cikin birnin Gombe, Gwamna Yahaya ya jaddada ƙudurin gwamnatin na ɗorewar tsaftar muhalli da kuma inganta rayuwar al’umma.
Ya buƙaci mazauna yankin da su tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na amfani da sabbin cibiyoyin tattara shara da kaucewa zubar da shara barkatai cikin magudanan ruwa, wanda ke ƙara janyo matsalolin muhalli musamman ambaliyar ruwa.
- Gwamnan Gombe Ya Gwangwaje Shugabannin Kananan Hukumomi Da Motoci
- Jihar Gombe Ta Rusa Kamfanin Zuba Jari Da Bunƙasa Ƙadarori
Gwamnan ya bayyana muhimmancin ɗaukar nauyi tare a kula da shara don hana ambaliyar ruwa da illolinta ga rayuka da dukiyoyi. Ya kuma sanar da fara aikin tsaftace manyan magudanan ruwa don tabbatar da kwararar ruwa ba tare da matsala ba, don kaucewa ambaliyar ruwa da kuma kare rayukan jama’a, dukiyoyi da ababen more rayuwa. Ya lura cewa zubar da shara barkatai a cikin magudanan ruwa na daga cikin manyan dalilan da ke janyo ambaliyar ruwa a cikin birnin, sannan ya jaddada muhimmancin ci gaba da wayar da kan al’umma game da illolin irin wannan ɗabi’a.
Gwamna Inuwa ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kiyaye muhalli ta hanyar sarrafa shara da kuma dasa bishiyoyi da yawa a fadin jihar. Haka kuma, ya sanar da gina ƙarin cibiyoyin tattara shara guda 21 ƙarƙashin shirin “Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes” (ACReSAL), a haɗin gwuiwa da Bankin Duniya.
Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Gombe (GOSEPA) za ta tabbatar da kwashe shara daga waɗannan cibiyoyi a kullum don samar da tsabta da ingantaccan muhalli.