A wannan makon mun zo muku da sabon salo, maimakon tattaunawa da Mabiya shafin Taskira, mai karatu da kai za mu yi. Sai ka kalmashe kafa ka gyara zama, mu je zuwa…
Sau tari idan zancen game da zamantakewar da ke tsakanin ma’aurata ya tashi, babban abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne, wace hanya namiji zai zama namiji, har ya mallaki akalar tafiyar da harkokin gidansa a matsayin maigida. Ko kuma wadanne hanyoyi ne mace za ta tsayu da kafafunta har ta mallaki mijinta, ko kuma wadanne hanyoyi ne za ta bi domin ta rike akalar miji har ta rika juya shi son ranta? Sanin irin wadannan kudurorin da galibi suke cikin zukatan ma’auratan ne ya sanya a yayin da aka wanke yarinya domin kai ta daki a matsayin amarya a ke yi musu huduba ta musamman kan yadda za ta zauna tare da mijinta.
Sai dai akwai bambanci wajen gabatar da irin wadannan hudubar. Idan mace ta tashi a gidan gargajiya, ma’ana gidan da aka fi son ta mallaki miji ko kuma ta zama gagarabadau ta yadda ba zai taba iya gindaya mata wasu sharuda na kashin-kansa ba a matsayin maigida, ko kuma kan batun kishiya da sauransu, sai a samu wata wadda za ta yi mata huduba ta musamman cewa, ‘Namiji ba dan goyo bane, don haka kada ta yarda ta bayar da kai bori ya hau.’
Hudubar ba daya ba ce a dayan bangaren. Misali, idan mace ta tashi daga cikin gidan Malamai yayin da za a yi mata hudubar bankwana, a kan fi jaddada mata cewa aure dai ibada ne, sannan a tuna mata cewa ibada kuwa ba a yinta da son rai ko lalaci.
A kuma tabbatar mata muddin tana bukatar tsira a duniya da lahira, to fa tilas ta yi wa miji biyayya dari-bisa-dari matukar bai kauce daga kan turbar shari’ar addinin Musulunci ba.
A nan, ba ina sukar ‘yan gargajiya ba ne, sai dai ina kokarin bayyana wasu daga cikin sirrukan zama tsakanin ma’aurata. Shin me ya sa namiji yake ji a ransa ba zai iya mallakar matarsa ba? Me kuma ya sa wasu matan ba sa la’akari da soyayyar farko da aka dora tafiyar a kai, suke bin wadansu hanyoyin ta bayan gida domin mallakar mazajensu?
Kenan za a yarda da ni idan na ce ma’aurata kan canza halayensu jim kadan bayan an daura musu aure. Idan har haka ne, mene ne musabbabinsu? Wasu manazarta wannan fanni sun tafi a kan cewa ba a samun isasshen lokacin da za a fahimci juna, a kuma fahimci irin tafiyar da ake fatan yi tare kafin a daura aure.
Abin da suke nufi a nan shi ne, akwai gazawa ainun a kowani bangare tsakanin iyayen miji da na matar musamman kan abin da ya shafi ilmi, ilmin kuma kan sha’anin aure.
Duk da cewa ana halartar makarantu, a kan saurari wa’azi daban-daban na zaman aure da sauransu, amma manazartan sun tabbatar cewa abu daya da aka fi yayatawa bangane da aure shi ne, ‘aure Sunnah’ ne, ko kuma a ce, Annabi (SAW) ya ce, ‘ku yi aure ku hayayyafa, domin na yi alfahari da yawanku a ranar gobe Kiyama.’
Shin ana samun lokaci isasshe wajen bayyana ainihin ‘Sunnar’ da ake zance a nan? Ko kuma wace hikima ta sa Manzo (SAW) ya ce ‘Ku hayayyafa domin na yi alfahari da yawanku ranar gobe Kiyama?’ Shin irin haihuwar da ake yi babu tsari, kuma tarbiyya ce Annabi (S) yake nufi? Ko wace iri? Wadannan su ne kadan daga cikin kalubalen da manazartan ke kallo a matsayin gazawar iyaye wajen ilmantar da ‘ya’yansu kafin su kulla auratayya a tsakaninsu.
Wasu kuma suna kallon matsalolin da ke aukuwa jim kadan bayan an yi aure a matsayin son duniya, wanda shi ne jigon wanzuwa cikin garari da bala’i daban-daban. Galibin ma’aurata kan dora akalar tafiyar da zaman aurensu ne kan son duniya musamman a wannan zamani. An wayi gari, hatta a zagayen wadanda ake gani Malamai ne a yau, ba a fi mayar da hankali kan aure domin Allah ba, sai abin da ake kira auren jari.
Shin mene ne auren jari? Me ya sa wasu ke hankoron auran mace domin a dan lasa musu dukiya ko wani abin duniya? A fili yake cewa duk wanda ya hau motar kwadayi, za ta sauke shi ne a tsakiyar tashar wulakanci. Amma duk da haka, abin alfahari ga wasu a ce yau sun auri ‘yar gidan wane ko kuma a ce ‘yarka na auren wani attajiri ko mai akalar mulki a hannu.
Baki dayan nazarin suna yin ishara ne kan abu guda, wato yadda ma’aurata da galibin al’umma ke jahiltar fasalin auren a farkon lokaci. Ko kuma idan aka tashi yin zance bangane da batun aure, sai a yi wa jama’a dabaibayi da cewa aure Sunnah ne. Kuma ba a zurfafa tunani kan mece ce Sunnar? Ba a yin bincike kan dalilan da suka sabbaba har fiyayyen halittun Annabinmu Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da tsarkakan iyalan gidansa da Sahabbansa managarta) ya bayyana aure a daya daga cikin manyan dabi’u. Har ya fada cewa, “Aure Sunnata ce duk wanda ya tozarta sunnata, ba ya tare da ni.”