Daya daga cikin babbar barazana ga Dimokuradiyyar ita ce, raunin jam’iyyun adawa, wanda mutane da dama na ganin hakan zai sa kasar ta kama tsarin jam’iyya guda daya.
A cikin tsarin mulkin dimokuradiyya, ‘yan adawa na matukar taka muhimmiyar rawa wajen kalubalantar gwamnati ta yadda za a gyara tsarin da bai yi daidai da tsarin mulkin dimokuradiyya ba. Ko da gwamnati ba ta yi amfani da kiraye-kirayen ‘yan adawa wajen gyara kuskure, tana amfana da su wajen gudanar da bincike a kan korafin da suka gabatar ta yadda za a samu damar yin gyara.
- Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukace Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
- Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Uruguay
Tsarin mulki na shugabancin kasa ya kawo ka’idoji ta yadda jam’iyyun adawa za su iya gudanar da bincike wajen gudanar da harkokin gwamnati.
A ko da yaushe, jam’iyyar adawa na sa jam’iyya mai mulki ta tashi tsaye wajen gudanar da tsare-tsare da kuma shirye-shiryenta. Haka nan kuma suna dakile wuce gona da iri da muguwar mulkin kama-karya.
A jamhuriya ta daya da ta biyu, Nijeriya tana da al’adar gudanar da siyasar adawa. Marigayi Cif Obafemi Awolowo na jam’iyyar ‘Action Group’ (AG), wanda daga ta koma jam’iyyar ‘Unity Party of Nigeria’ (UPN), a matsayinsa na dan adawa, ya tunkari gwamnatin da ke kan karagar mulki da hujjoji masu tsauri da alkaluma ta yadda za a ceto Nijeriya. Hatta Dakta Nnamdi Azikiwe da sauran su duk ’yan adawa wadanda suke kalubalantar wuce gona da iri na jam’iyya mai mulki da ke rake da gwamnati.
Ko a lokacin mulkin soja, an sami manyan kungiyoyin fararen huda kamar irin su ‘Campaign for Democracy (CD)’, ‘Mobement for National Reformation (MNR)’, kwamitin kare hakkin Dan’adam (CDHR), kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA), kungiyar kwadago (NLC) da dai sauran su, sun yi tsayan daka wajen yakar mulkin kama-karya da rashin gudanar da mulki yadda ya kamata.
Irinsu Cif Gani Fawehinmi, Farfesa Wole Soyinka, Aka Bashorun, Olisa Agbakoba, Femi Falana, Beko Ransom-Kuti, Ayo Obe, Ken Saro-Wiwa da dai sauransu sun shiga gidan yari saboda sukar gwamnati.
Amma a yau a siyasar Nijeriya babu wata adawa mai karfi da yadda zai iya kawo sauyi ga manufofin gwamnati wadanda ba dace da tsarin mulki ba. Tun bayan kammala zabukan da suka gabata, jam’iyyun adawa sun yi barci, lamarin da ya sa jam’iyyar APC mai mulkin gwamnatin tarayya take jagorantar ‘yan Nijeriya yadda take so.
Yanzu haka dai a Nijeriya manyan jam’iyyun adawar sun hada da jam’iyyun PDP da LP, amma babu daya daga cikinsu da ta iya kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki yadda ya kamata a wurin gudanar da mulkin Nijeriya.
A yanzu haka dai, ‘yan Nijeriya sun zura ido don ganin yadda PDP da LP za su iya amsar mulki a hannun jam’iyyar APC.