A ƴan kwanakin nan ne, jarumai daga masana’antar Kannywood, waɗanda a baya suka samu ɗaukaka tare da samun ɗimbin dukiya a masana’antar ta shirya fina-finan Hausa, suka koka a kan yadda duniya ta juya musu baya.
Ko shakka babu, waɗannan jarumai sun yi matuƙar samun alhairai da masoyan daban-daban a wancan lokaci. Ɗaya daga cikin jaruman ita ce, Ummi Nuhu, wadda a shekarar 2000 zuwa 2015, tana ɗaya daga cikin manyan-manyan waɗanda ludayinsu yake kan dawo a masana’antar.
- Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ
- Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
Ummi Nuhu, wadda iyayenta ‘yan asalin garin Bunkure ne da ke Jihar Kano, amma aka haife ta; ta kuma tashi a Jihar Kaduna, a shekara ta 2000; tauraruwarta ta fara haskakawa a Kannywood, a ƙarƙashin jagorancin Ali Nuhu, ta yi fice a fina-finai da dama da suka haɗa da; Al’amari, Fil’azal, Zo Mu Zauna da kuma Rabin Jiki, inda ta zama ɗaya daga cikin fitattun jarumai na Kamfanin FKD.
Amma daga baya, ta ɓace ɓat; an daina ganin fuskarta a shirin fina-finan Hausa na Kannywood, wannan ne dalilin ma da ya sanya masu sha’awar kallon fina-finan na Hausa a yanzu, ba su san ta ba. Kwanakin baya, jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta yi hira da ita a cikin shirinta na ‘Gobon’s Room Talk Show’, a wannan shiri ne, Ummi ta bayyana batutuwa da dama dangane da rayuwarta a lokacin da take kan sharafinta da kuma lokacin da aka daina yayinta.
Haka zalika, Ummi a wata hira da ta yi da BBC Hausa, ta bayyana yadda ta yi da-na-sanin wasu abubuwa da dama da ta aikata a lokacin da kan ɗaukaka da tarin masoya, “Na yi lokacin da babu wani Furodusa da zai yi fim, ba tare da ya nemi na fito a cikinsa ba, a wancan lokacin; na samu damammaki masu ɗimbin yawa da suka haɗa da kuɗaɗe, daukaka ta masoya, har ta kai ga duk inda na shiga sai na haɗu da masoya maza da mata, suna ɗokin zuwana wannan waje”, in ji Ummi.
“Na taɓa zama abar kwatance, musamman a ɓangaren da shafi kuɗi, suna, girmamawa, amma kuskuren da na yi ya zama dalilin da yasa masana’antar ta juya min baya, sakamakon babu abin da na iya ko na sani face; harkar ta fim. Halin da ake ciki yanzu, babu wani tallafi, babu aikin yi, akwai lokacin da ina da ɗimbin masoya da suke son aurena da kuma nuna min soyayya, amma sai na kasa zaɓen wanda zan ci gaba da rayuwata da shi a wancan lokaci.
Babban dalilin da ya jawo min koma-baya a harkar fim shi ne, hatsarin da na samu na mota, wanda Allah ya jarrabce ni da shi, na yi hatsarin mota da har sai da na samu karaya huɗu a ƙafata, sannan kuma na samu buguwa a kaina da har sai da na manta da komai na rayuwa da na sani a wancan lokaci, bugu da gari; fuskata ta samu raunuka masu yawa da suka canza mani fasalin fuskar tawa, hakan ya sa na ɗauki tsawon lokaci ina jinya.
Da ta ke amsa tambaya a kan ko ‘yan’uwan sana’arta na Kannywood sun taimaka mata a lokacin da take cikin wannan mawuyacin hali? Ummi ta ce, duk da babu wani wanda ya ɗauki nauyin jinyarta a wancan lokaci, amma dai ba za ta taɓa mantawa da yadda suka riƙa zuwa har gida suna gaishe ta ba, “Ni na ɗauki nauyin jinyar kaina, saboda bakin gwargwado ina da abin da zan iya ɗaukar nauyin jinyata”, in ji Ummi.
Dangane da da-na-sanin da ta ke yi a rayuwa kuma, Ummi ta ce; babu wani abu da take da-na-sanin rashin yi da ya wuce aure, domin da a ce ta yi aure, zuwa yanzu wataƙila da Allah ya azurta ta da samun zuri’a, waɗanda za su riƙa kula da ita yanzu da kuma bayan ta tsufa. “Don haka, ina fatan yin aure kafin rayuwata ta zo ƙarshe”.
Daga ƙarshe, tsohuwar jarumar ta buƙaci matasa masu tasowa a masana’antar Kannywood, da kada su maimaita irin kuskuren da da yawa daga cikin tsoffin jarumai mata suka yi, “Ina shawartar duka wata mace mai lokaci a masana’antar Kannywood yanzu, da ta tabbatar da cewa; ta saka hannun jari a wasu wuraren kasuwanci da za su riƙa samar mata da wani abu ta yadda ko da lokacin ɗaukakarta ya wuce, za ta ci gaba da yi; domin kula da rayuwarta.
Dalili kuwa shi ne, duk irin ɗaukakar da kika samu a yanzu, lokaci na nan zuwa da dole zai gushe, ki zama kamar ba ki taɓa samun wannan ɗaukaka ba, kamar yadda yanzu ake yi babu mu, duk kuwa da irin shaharar da muka samu a lokutan baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp