Ministan Ma’aikatar Sufurin Jiragen Kasa, Mu’azu Sambo, ya bayyana cewa babu wata gwamnati a kasar nan da ta yi aikin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi a kasar nan.
Sambo wanda ya sanar da hakan a jiya Juma’a ya kuma yi Ikirarin da cewa, makiyan Buhari sun tabbatar da cewa, Gwamnatin ta samar da ayyukan ci gaba a kasar duk da cewa, Gwamnatin na fuskantar kalubalen rashin tsaro a kasar.
- “Korar Fulani A Edo: Ina Ake So Wadanda Aka Haifa A Jihar Shekara 50 Su Koma?”
- Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak
Ministan, ya sanar da hakan a jihar Legas a wani zagayen duba aikin tashar layin Dogo Mobolaji Johnson da kuma kaddmar da hanyar layin Dogo daga Legas zuwa garin Ibadan.
Sambo wanda aka nada a mukamin na Ministan Ma’aikatar a kwanan baya ya je jihar ce domin duba ayyukan hukumomin da ke a karkashin ma’aikatar ta Sufurin.
Ya nuna gamsuwarsa kan kayan aikin da aka samar na ci gaba a fannin, sai dai ya ce, akwai sauran aiki da dama, da ya kamata ayi wajen samar da kayan aikin.
Sambo ya kuma nanata kudurin Gwamnatin Tarayya na cewa, ba za a ci gaba da jigilar fasinjojin daga Abuja zuwa Kaduna ba, har sai an sako fasinjojin da masu garkuwar suka sace a ranar 28 ga wata Maris na 2022 tare da kuma kara tabbatar da tsaro a hanyar.