Shahararren Mawakin Hausa, Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara, yana fuskantar neman kuɗin fansa har Naira miliyan ₦900m domin a sako mahaifiyarsa da aka sace.
Wata majiya mai tushe a garin Kahutu da ta buƙaci a sakaya sunanta ta shaida wa Jaridar Aminiya cewa tun da farko masu garkuwar sun bukaci Naira Biliyan ₦1b ne amma sun rage zuwa Naira miliyan ₦900m bayan tattaunawa.
- Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Zuwa 4 Ga Watan Yuli
- Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Zuwa 4 Ga Watan Yuli
Majiyar ta yi ƙarin bayani cewa ƴan bindigar sun tuntuɓi iyalan ta hanyar amfani da wata wayar da suka ɗauka a yayin garkuwa da su. Sun dage sai sun yi magana da shi kansa Rarara, amma daga ƙarshe sun amince su tattauna da wani ɗan uwansa bayan sun samu labarin rashin lafiyarsa bayan faruwar lamarin.
Waɗanda suka yi garkuwa da su sun tabbatar da cewa Hajiya mahaifiyar Rarara na cikin ƙoshin lafiya kuma sun yi alƙawarin sakin ta bayan sun biya kudin fansa.
Duk da haka, bayan ƴar gajeren tattaunawar farko, ƴan bindigar ba su sake kira ba, sun bar iyalin suna jiran ƙarin tattaunawa don ci gaba da neman ragi.
Kauyen Kahutu gaba daya sun shiga cikin kaɗuwa dangane da sace Hajiyar wace ta yi suna wajen karamci da taimakon iyalai da marayu da dama a yankin.