Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin dake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
   Tsokacin mu na yau zai yi duba game da al’adar Malan Bahaushe na Tashe, wanda Hausawa suka saba gudanar da shi a kowacce shekara cikin wata mai albarka na Ramadana, a yayin da wata ya cika kwana goma kenan. Ana fara tashe a farkon goma ta biyu wato goma na wuya, kamar yadda Malan Bahaushe ya rarraba sunan; Goma Na Marmari, Goma Na Wuya, Goma Na Dokin Sallah.
    Sai dai abun dubawar a nan shi ne, a wannan lokacin al’umma na cikin wani hali na kuncin rayuwa, wanda hakan ka iya janyo rashin gudanar da tashen yadda ya kamata, kamar dai yadda aka saba yi a baya. Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin Taskira game da wannan batu; Ko mene ne Tashe? Ya ake gudanar da Tashe? Su wa ya kamata su yi Tashe? Ko ya Tashen bana yake kasance?
   Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aminu Adamu Malan Madori A Jihar Jigawa:
To tashe wata dadaddiyar al’ada ce ta malan bahaushe wadda ake gudanar da ita a cikin tsakiyar watan lamarana, tashe ya kunshi mu’amula da al’adun malan bahaushe masu ban sha’awa, ana gudanar da shi ne domin nishadantar da al’umma, kuma yara mata da maza da matasa sune suke gudanar da shi wanda suke bi gida-gida kwararo-kwararo wajen gudanar wa. To tashe ana gudanar da shi kamar wasan kwaikwayo ko drama kuma ana kwaikwayon wasu al’adun malan bahaushe dama mu’amular sa ta yau da kullum wajen shirya tashe, a wasu lokutan tashe yana kunsar fadakarwa ga al’umma ko nishadantarwa da kuma tunawa al’umma tsofin al’adun malan bahaushe. To wadanda ya kamata su yi tashe sune; yara mata da maza, matasa maza da mata dama dattawa wadanda suka ga jiya da yau domin farfado da tsofin al’adun malan bahaushe da suka bata. To hakika wannan shekara ana cikin mawuyacin hali da tsadar rayuwa, don haka tashe daya kamata ayi shi ne wanda nunawa mutane, juriya, hakuri, tashi tsaye wajen neman na kai da kuma gudanar da ayyuka nagari da addu’a har Allah ya kawo mana saukin wannan matsala ta tsadar rayuwa da tsananin talauci dake addabar al’umma. To batun tashen daya ke burge ni shi ne “ka yi rawa kai malam – kayi rawa ban yi ba”, domin yana nuna martabar malan ya fi karfin a same shi yana rawa, yana nuna malamai mutane ne masu kima da daraja a cikin al’umma don ba sa son duk wani abu da zai taba darajar su a idon al’umma. To ya kamata masu tashen su bi a hankali domin mutane suna cikin wani yanayi, kuma ya kamata su gudanar da shi cikin tsafta da bin doka da oda, daga nan nake addu’ar Allah ya maimaita mana.
Sunana Hadiza Muhammad, Daga Garin Gusau Ta Jihar Zamfara:
Tashe wani wasa ne da ake gudanarwa lokacin azumi, ana fara shi ne in azumi ya kai sha biyar ko ashirin. Ana gudanar da shi ta hanyoyi da dama, ta hanyar kade-kade da wake-wake, wasu su kan gudanar da shi a cikin siffar wasan kwaikwayo. Mafi yawanci yara ne suka fi yin tashe maza da mata, amma a wasu lokkutan har manya kan dan taba, sai dai yara ne ya fi kamata a ce sun yi tashe. Gaskiya tashen bana zai zo da kalubale, duba da yanayin halin da ake ciki, abun da mutane suke da shi baya isarsu, bare har su aje na ba masu tashe. Tashen daya fi burge ni shi ne wanda ake cewa; “Iya talgenki na zuba”, ita kuma sai ta ce “Yi maza karkada mini, kin san tankade ni kai”. Yadda tashen yake shi ne; Yarinya daya za ta zauna tana kwatanta kamar tana tankade da rariya, su kuma sauran yaran suna tsaye suna yin wakar iya talgenki na zuba, ita kuma tana amsa musu. Shawarar da zan ba masu zuwa tashe shi ne, kada su sa ma ransu dole sai sun samu abubuwa kamar yadda aka saba, in sun samu su gode, in da ba a basu ba kar su ga laifin su, su kuma wadanda za a je mawa, kar su fake da halin da ake ciki su mai da abun rowa, kalilan din da ka ke da shi ka sanmusu ko ya yake, dan taimaka wa wannan dadaddiyar al’ada ta dore.
Sunana Sadi Dauda Baturiya, Kirikasamma A Jahar Jigawa:
Shi dai tashe wani wasa ne daga cikin jerangiyar wasannin al’adu na malan bahaushe daya saba yinsa, wanda ‘ya’yan Hausawa suka saba yinsa daga goma ga wata zuwa sha biyar ga watan Ramadan. Wasan tashe dai mafi yawa yara kanana ne ke yi wato ‘yan mata da samari, ba manyan mutane ba. Duk da cewa yanzu lokaci ne na hanyoyin sadarwa cikin sauki wato muna ga yadda bidiyon manyan mutane ma suna yi ya danganta da waje da kuma yanki. Shi dai tashe yanada nau’ika daban-daban mafi duk nau’in da za ai na tashe yanada shigar sa ta daban, musamman ma al’ummar mu na kauye su suka fi kwarewa a wannan fanni na tashe. Mafi yawan tashe dai an fi yin sa a cikin gidaje da kwararo-kwararo da lunguna na gari ko anguwannin da ake ciki ana yin sa cikin raha da nishadi tare da farin ciki, duk da cewa a wani lokacin akwai zambo da yakuce a cikin taken tashen, ya danganta da salo ko nau’in tashe da masu tashen suka zabi yi. Eh to, a gaskiya tashen bana za a yi shi ne domin cike gibin al’adah’ duba da yanayin da ake ciki, na farko dai shi ne; fatara da talauci da ake fama da shi a duniya musamman kasashenmu, na biyu kuma shi ne; a zamanin yanzu kullum wasannin al’adu na malan Bahaushe kara dakushewa suke ta hanyar yadda ke zuwa da sabbi ko bakin al’adu na aro, wasu ma basu da tushe, wadannan dalilai suka sa a zahirin gaskiya tashen bana ba zai yi armashi da tasiri kamar na shekarun da suka gabata ba, wato dai ana cikin wani yanayi da masu iya magana suka ce in duka yai yawa na kai kawai ake iya karewa. To mudai a lokacin ta mu yarintar wato lokacin da mukai namu tashen mun fi kwarewa a wani tashe da ake cewa; “yaran Malan kar ku fadi in ku ka fadi za mu ji kunya”, duba da cewa mu a gidan almajirai muka fito irin wannan tashen muka fi yi. In zan bada shawara ga masu tashe a wannan shekara shi ne; su yi wa Allah su guji yin salon tashen da zai taba natija da mutuntaka irin ta al’adun Malan Bahaushe domin kuwa ba shi ne salo ko gwadabe da tirgada malan Bahaushe ba a cikin salon tashe.
Sunana Hafsat Sa’eed Jihar Kebbi:
Wasan tashe wata al’ada ce da ake yi a kasar Hausa a lokacin azumin watan Ramalana, inda matasa har ma da yara kan yi shiga kala-kala, suna kida da waka. Tashe hanya ce ta fadakarwa, ilmantarwa da kuma ankarar ko nusar da mutane game da wasu batutuwan da suka shafi rayuwa, kuma hanya ce ta nishadantar da masu azumi don su manta da gajiyar da suke tare da ita. Ana amfani da tashe wajen tashin mutane daga barci domin su yi sahur, sannan a kan sallami masu tashe da kudi ko hatsi da dai sauransu. Yara ne suke yin tashe da kuma matasa, a tunani na tashen bana za a yi shi ba kamar yadda aka saba ba sabida halin kuncin da ake ciki na rayuwa. Tashen dana sani akwai “Malama ga kudin toshinki”, bankada lefe na ki zuba mun, ba na barin sallah ta wuce ni”. Shawarar da zan ba wa masu tashe shi ne; su yi tashe me nagarta, cikin hikima da fusaha ban da zage-zage ko cin mutuncin wani, ban da zagin shuwagabanni. Sannan su ma wadanda aka je wa su yi hakuri musamman halin da ake ciki dan wasu sai sun kai duka ko zagi, su yi hakuri su bar yaran su yi idan kuma ba sa son hayaniya su ba su hakuri.
Sunana Muhammad Najib Muhammad Sansani, Miga LGA Jihar Jigawa:
Tashe dai wani wasa ne da ake yin sa a kasar hausa musamman lokacin da kayan gona suka iso gida ma’ana da Kaka kenan, Ana gudanar da tashe ta hanyar kirkirar wani wasa da zai kayatar da mutane sai ana bi gida-gida ko kasuwannici rumfa-rumfa ana aiwatar da wannan wasa. Wadanda suka kamata su aiwatar da wannan wasa sune ‘yan mata, samari da kuma kananan yara.Tashen bana zai kasance marar kayatarwa duba da yadda rayuwar ta ke gudana matsalolin rashin kudi sun yi yawa domin ba kowa ne zai ma tsaya yana ganin wasan ba, dan kar ya bayar da ‘yar kwandalarsa. Wasan tashen da ya fi burge ni shi ne “iya ga barawon ice”. Shawarata daya ce; ya kamata a matsayin mu na hausawa mu kara rike abubuwa na aladar mu.
Sunana A’isha Abdullahi Muktar Hadejia A Jihar Jigawa:
Tashe wata al’ada ce da ake yin ta yayin da ake yin ibadah ta azumi a cikin watan Ramadan, ana gunar da tashe ne da safe koda dare. Matasa maza da mata yara, sune suke gudanar da tashe. Da yake al’ada ce mai takaitaccen lokaci hakan ba zai hana yin tashe ba, duk da tsadar rayuwa da ake ci sai dai ba lallai a sami kwatankwacin abin da ake samu a baya ba. Tashen da ake yi za ai shigar tsofi da fatanya a hannu yana gwada noma ana cewa; “Baba da aiki ke ke”, shi kuma zai ce danma na tsufa, Baba tsaya ka huta, sai na kai kunya”. Tashen na nuna juriya irinta manya kuma duk da girma bai hana shi nema ba. Shawarar da zan bawa masu tashe shi ne; “Dan Allah su yi hakuri da abin da za a basu, koma basu samu ba sun raya al’ada, kuma dan Allah kar suna damun al’umma da kade- made, wanda aka je wa kuma su yi hakuri ko yaya ne ana bawa masu tashe ba sai da yawa ba, kasancewar kowa ya san halin da ake ciki ban da kyara da fadar magana.
Sunana Babangida Danmama Malam Madori Jihar Jigawa:
Tashe a kasar Hausa wata dadaddiyar al’ada ce ta bahaushe, wacce ake danganta ta da al’adunsa masu nasaba da addini, mafi yawan tashe ana fara shi ne a yayin da watan azumin ramadan ya yi kwana goma. Yadda ake tashe asali ‘yan mata da samari ne ke aiwatarwa a cikin watan azumin ramadan, da nufin tashin masu barci domin tashi sahur. ‘Yan mata da samari da kananan yara ne suke tashe cikin shiga ta ban dariya suna yawo kwararo-kwararo lungu-lungu a unguwanni da kasuwanni suna nishadantar da mutane da abubuwan barkwanci. Tashen bana zai samu karancin masu yi, sabanin baya da ake sosai domin a samu kudi saboda wannan yanayi da aka tsinci kai na tsadar rayuwa da karancin kudade a hannun mutane. Tashen Macukule shi ne tashen da ya fi burge ni, sannan shi wannan tashe wani mutum ne ke daura kasusuwan dabba a jikinsa, yana waka yana yabawa naman kare ta hanyar bayyana dadin naman. Shawarata ga wadanda ke gudanar da tashe ita ce; su gujewa cin mutuncin mutane ko yin wani abu da zai taba al’adar bahaushe ko addini, sannan su kansu wadanda ake zuwa a yi musu tashen yana da kyau suna kyautatawa masu yi domin karfafa musu gwiwa.
Sunana Zainab Zeey Ilyas, Jihar Kaduna:
Tashe dai wata al’ada ce da hausawa ke gudanar da ita duk shekara a goma ta biyun watan musulunci na ramadana, kuma abu ne da yake sanya mutane farin ciki da annashuwa. Ana gudanar da tashe ne ta hanyar da yara suke shiga cikin gidajen mutane ko kuma a unguwanni, yayin da suke yin shiga ta ban dariya ya danganta da yanayin tashen da za su yi. Wadanda ya kamata su yi tashen sune; yara marasa azumi kuma masu yawan bada dariya wadanda suka iya da kwarewa a tashe, amma asalin masu yi su ne; yara da matasa har ma da manya, maza da mata. A gaskiya ni a ganina ba abun da zai kawo tsaiko a tashen bana, domin tashe ba abun da ya hada shi da tsadar rayuwa, sai dai in suna jin yunwa ba za su samu kuzarin yin wannan tashen ba da kuma kayan da za su sanya a jikinsu, domin bada dariya ba za su yi kamar baya ba. Ni dai tashen da ya fi burge ni shi ne; “Malama ga kudin toshinki, Ban kada lefe na ki zuba min bana barin sallah ta wuce ni”. Mata ne za su zo su ajjiye kaya sai su ware wata macen da za ta rika baitin, sai a nuno ta za ta yi sallah sai su dinga kida da amshin. Shawarar kuma da zan bawa masu gudanar da tashe ita ce; kar a je garin yin wasa a saka kai cikin kasada, a kiyaye.
Sunana Kabiru Hassan Malammadori, Faga Jihar Jigawa:
Tashe wata al’adar Hausawa ce wadda ake yin ta a kasar hausa bayan kowane kwana goman (10) farko na watan azumin Ramadan a kowace shekara. Yadda ake yin tashe, matasa har ma da yara kan yi shiga kala-kala, suna kida da waka da nufin fadakarwa, ilmantarwa, nishadantarwa ko nusar da mutane game da wasu batutuwan da suka shafi rayuwa. Samari, ‘yan mata da kananan yara ne ya kamata su yi tashe. Tashen bana zai samu taskaro duba da yadda rayuwa ta yi tsada. Tashen NA’LAKO ya fi birge ni, shi wannan tashe yadda ya ke, mutum daya ne zai fito a matsayin Na’lako tare da tawagarsa suna zagayawa suna waka suna cewa “Dare da yawa! haka ma rana da yawa ‘yan samari! wasa muka zo ba fada ba munzo mu kama gwagware”. Ina bawa masu tashe shawara da su guji cin zarafi ko kuma yin abin da zai taba al’ada da addinin hausawa, su kuma wadanda ake zuwarwa su karbi abin hannu biyu su karfafawa masu yin tashen gwiwa.