Kocin ƙungiyar ƙwallon ta Kano Pillars, Usman Abdullahi, ya ajiye aikinsa, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a shafinta na X (tsohon Twitter).
Usman ya shafe kusan shekaru biyu yana horar da Pillars tun bayan da ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru uku.
- EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna
- Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Mai A Legas
A cikin sanarwar, ƙungiyar ta ce, “Muna tabbatar da cewa kocinmu, Usman Abdullahi, ya sauka daga muƙaminsa saboda dalilan kansa.”
A watan Fabrairu da ya gabata, Kano Pillars ta dakatar da Usman daga aiki na tsawon makonni biyar saboda rashin sakamako mai kyau, da kuma wasu kalaman da ya yi ga magoya bayan ƙungiyar bayan wasan da suka tashi babu ci da Bayelsa United a mako na 22 na gasar NPFL.
Usman Abdullahi ya taba horar da manyan ƙungiyoyi irin su Enyimba da Wikki Tourists ta Bauchi.
Haka kuma, ya taɓa zama mataimakin kocin Super Eagles lokacin da Jose Peseiro ke jan ragamar ‘yan wasan Nijeriya.
A kakar bara ta NPFL, ya jagoranci Kano Pillars ta ƙare a matsayi na 9.
Ko da yake Usman bai bayyana cikakken dalilin saukarsa ba, masu sharhi a wasan ƙwallon ƙafa na ganin matsin lamba daga magoya baya da rashin nasara sun taka rawa.
Har yanzu, ƙungiyar ba ta fitar da sabuwar sanarwa kan wanda zai maye gurbinsa ba.
Masu sha’awar wasan ƙwallon ƙafa a Kano na fatan za a kawo sabon kocin da zai dawo da martabar Pillars a wasannin gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp