ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane

by Sadiq
1 year ago
APC

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta ce za ta ɗauki matakin shari’a kan jam’iyyar PDP saboda zargin da ta yi wa Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, da hannu a satar mutane a jihar.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

  • Yadda Kasar Sin Ta Zo Da Sabon Salon Zamanantar Da Sashen Jigilar Kayayyaki
  • An Gudanar Da Taron Ministoci Masu Daidaita Ayyukan Da Aka Amince Yayin Taron FOCAC

A cewarsa, zargin da Mustapha Jafaru Kaura, mai magana da yawun Gwamna Dauda Lawal, ya yi, ba su da tushe, siyasa ce kawai.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta fito ne bayan taron gaggawa da kwamitin aiki na jam’iyyar APC a jihar ya gudanar karkashin jagorancin Hon. Tukur Umar Danfulani, inda suka tattauna batun wata hira da Kaura ya yi a wani bidiyo da aka yaɗa a yanar gizo.

A hirar, Kaura ya yi iƙirarin cewa satar ɗaliban makarantar sakandare ta Kankara a Jihar Katsina da aka yi a ranar 11 ga watan Disamban 2020, an tsara ta ne da sanin Matawalle.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal.

APC ta ƙaryata wannan zargi.

Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa.

Jam’iyyar APC ta ƙalubalanci Kaura da ya kawo hujjoji kan wannan zargi da kuma wasu mutane da aka sace a jihar, kamar satar ɗalibai mata 270 daga makarantar Government Girls Secondary School da ke Jangebe a ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, da kuma satar ɗaliban Kwalejin Noma da Kiwo da ke Bakura.

APC ta jaddada cewa gwamnatin Matawalle ta yi ƙoƙari wajen yaƙi da ‘yan bindiga da ceto al’ummomi da dama.

Ta bayyana yankuna kamar Gwaram, Kanoma, Kaya, Faru, Janbako, Lilo da Anka, a matsayin wuraren da aka gudanar da ayyukan tsaro da taimako.

Jam’iyyar ta kuma ce tana duba yiwuwar ɗaukar matakin shari’a kan gidan talabijin na Maibiredi TV da ya watsa hirar da ake ganin an shirya don ɓata sunan ministan.

Ta zargi PDP da ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga gazawarta ta hanyar yaɗa ƙarya da tayar da fitina don samun moriyar siyasa.

A ƙarshe, APC ta yi kira ga mambobinta da su zauna lafiya da bin doka, inda ta bayar da tabbacin cewa gaskiya za ta fito fili, kuma za a yi adalci.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Ya Kamata Ana Kammala Shari’ar Zaɓe Kafin Rantsuwa

Ya Kamata Ana Kammala Shari'ar Zaɓe Kafin Rantsuwa

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.