Kasashen Nahiyar Turai za su san takwarkoinsu da za su fafata neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da su a cikin wannan satin a birnin Zurich na kasar Switzerland wanda kuma haka ne zai bayar da damar fara buga wasannin neman cancanta.
Kasashen Turai 16 ne za su samu gurbi a gasar wadda aka fadada zuwa kasashe 48 da za a yi a Amurka da Canada da kuma Medico bayan da aka sauya tsarin yadda ake neman gurbin Nahiyar Turan, an kara yawan rukunai, sannan an yi kanana sama da na baya.
- Minista Da Darakta Janar Na VON Sun Yi Alhinin Rasuwar Babbar ‘Yar Jarida, Rafat Salami
- An Yi Bikin Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Telabijin Na Habasha Da Sin
Za a samar da rukunai 12 da za su yi wasannin neman gurbi. Kununai shida za su kasance da kasashe hudu, yayin da sauran shidan za su zama suna da biyar-biyar kuma tawagogin za su fafata da juna gida da wajen kamar yadda aka saba.
Duk tawagar da ta yi ta daya a kowanne rukuni za ta zama ta samu tikitin Kofin Duniyan, yayin da na biyu za su buga wasannin neman cike gurbi sannan kuma har ila yau za a dauki kasashe hudu cikin 16 da za su yi wasan neman gurbi a gasar.
Ko wanne rukuni zai kasance da tawagar guda daga cikin kowacce tukunya hudu. Rukunai shidan za su zama suna da tawaga guda daga tukunya ta biyar. Akwai iyaka ta wacce tawaga ce za ta kasance a kowanne rukuni, da kuma wanda za ta fafata da shi.
Za a fitar da tawagogin bisa tsarin tukwanen da ke da akwai, sai an fara da tawagogin tukunyar farko sannan ta biyu har zuwa ta karshe kamar yadda yake a tsare a yadda ake raba jadawalin gasar cin kofin na duniya.
Tukunya 1: Spain, Germany, Pkotugal, France, Italy, Netherlands, Denmark, Croatia, England, Belgium, Switzerland, Austria. Tukunya 2: Ukraine, Sweden, Turkey, WALES, Hungary, Serbia, Poland, Greece, Romania, Slodaakia, Czech Republic, Nkoway.
Tukunya 3: SCOTLAND, Slodaenia, Republic of Ireland, Albania, Nkoth Macedonia, Gekogia, Finland, Iceland, NKOTHERN IRELAND, Montenegro, Bosnia-Herzegodaina, Israel Tukunya 4: Bulgaria, Ludembourg, Kosodao, Belarus, Armenia, Kazakhstan,
Azerbaijan, Estonia, Cyprus, Faroe Islands, Latdaia, Lithuania Tukunya 5: Moldodaa, Malta, Andkora, Gibraltar, Liechtenstein, San Marino
Su wane ne za su kasance cikin rukunin tawaga hudu?
Tawagogi hudu da suka je wasan kusa da karshe a watan Maris za su tafi rukuni dai-dai na neman gurbin gasar Kofin Duniya daga rukunin A zuwa F kuma wannan saboda an buga wasannin ne a watan Yuni, ba kuma a samu damar wasannin share fagen kofin Duniya a lokacin ba.
An dai raba jadawalin ne a gabanin fara wasannin, wadanda suka je wasan kusa da karshen za su zama kamar masu rikon wuri ne, misali kamar gwarzuwar gasar Faransa za ta samu rukuni sai Croatia itama da kuma sauran kungiyoyi biyun karshe.
Shin akwai wani haramci a gasar?
Saboda dalilai irin na siyasa, Ukraine da Belarus ba za su kasance a rukuni guda ba, kazalika Gibraltar da Sifaniya. Dole sai an raba Kosodao da Serbia da kuma Bosnia-Herzegodaina daga rukuni daya domin kaucewa rikicin siyasa.
Yanayin gari ka iya zama wani dalilin shi ma, saboda yiwuwar sanyi Estonia da kuma wasu kasashe biyu ne za su iya zama a rukuni daya da suka hada da Faroe Islands, Finland, Iceland, Latdaia, Lithuania da Nkoway.
Ba za a hada Iceland da tsibirin Fkooes wuri guda ba saboda ana musu kallon kasashe biyu da yanayinsu ke da hadari. Sannan akwai kuma yanayi na yankunan da kasashe suka fito, kamar Kazakhstan da Azerbaijan da kuma Iceland ba za su hadu da juna ba saboda nisan da ke da shi na tafiya zuwa Turai.
Yaushe ne za a fara wasannin?
Za a yi wasannin ne guda 10 yayin hutun kasashe da za a samu sau biyar kuma za a yi hutun ne a tsakanin 21 zuwa 25 ga watan Maris, sai 6 zuwa 10 ga watan Yuni, akwai 4 zuwa 9 ga watan 14 ga watan Oktoba sai kuma 13 zuwa 18 ga watan Nuwambar shekara mai zuwa.
Babu wata tawaga da za ta buga wasanni a duka wadannan lokutan hutu saboda wasanni bakwai kawai aka amince a yi sannan wasu tawagogin za su fara a watan Maris wasu kuma a Yuni, amma tawagogin da za a raba a rukunai hudu sai a watan Satumba za su fara nasu wasannin.
Wasannin cike gurbi kuma za a yi su ne a tsakanin 26 zuwa 31 ga watan Maris din 2026.
Yaushe za a yi Kofin Duniya?
Za a fara Kofin Duniya a ranar 11 ga watan Yuni a birnin Medico za a kuma a kammala a ranar 19 ga watan Yuli a birnin New Jersey kuma an fadada gasar zuwa kasashe 48 daga 32, kuma za a kwashe kwana 39 ana gudanar da gasar.
Sabon tsarin zai hada da rukuni 12 da yake dauke da tawagogi hudu ciki, kuma tawagogi 32 da za su yi saura za su je matakin sili daya kwale.