Abba Ibrahim Wada" />

KOFIN DUNIYA: Ingila Tana Dab Da Kafa Tarihi A Duniya

Tawagar kwallon kafa ta mata ta kasar Ingila, ta kai daf da wasan karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Faransa, bayan da ta doke kasar Norway daci 3-0 a birnin Le Habre dake kasar Faransa a  ranar Juma’a.

Jill Scott ce ta fara cin kwallon, sai Ellen White ta kara ta biyu kuma ta biyar da ta ci a wasannin bana sannan Lucy Bronze ta kara ta uku wanda sakamakon hakan yasa yanzu suka samu tikitin matsawa mataki na gaba a gasar ta duniya

Tawagar ta Ingila ta zama ta farko da ta kai karawar daf da karshe a manyan wasa biyu a jere, bayan da ta kai daf da karshe a kofin duniya a 2015 da kuma ta nahiyar Turai wato Euro 2017 duka a karkashin mai koyarwa Phil Nebille.

“Nayi farin ciki da wannan masara da muka samu saboda babban burina shine kafa tarihin da babu kamarsa a kasar Ingila kuma inada kwarin guiwar cewa ‘yan wasa na sun shirya domin bawa duniya mamaki” in ji Phil Nebille, tsohon dan wasan Manchester United

Ya cigaba da cewa “Yanzu babban burina shine zuwa wasan karshe wanda nake fatan zamu samu kuma wannan ne lokaci mafi farin ciki a rayuwata ta koyarwa a duniya saboda nasamu nasarar da ban taba samu ba”

Ingila za ta buga wasan kusa dana karshe da wadda ta yi nasara a fafatawa da za a yi yau Asabar  tsakanin mai masaukin baki kasar Faransa da mai rike da kofin wato kasar Amurka ranar 1 ga watan Yuli.

Exit mobile version