Babban kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya amince cewa zai yi wuya a shawo kan matashin dan wasan gaban Arsenal Ethan Nwaneri ya buga wa Nijeriya wasa, an haifi Nwaneri a Kasar Ingila amma kuma mahaifinshi dan Nijeriya ne yayin da mahaifiyarsa ta ke ‘yar Ingila.
Dan wasan mai shekaru 18 ya riga ya bugawa Ingila wasa amma har yanzu yana iya sauya sheka zuwa Nijeriya, Chelle ya yi ikirarin cewa kocin tawagar Ingila da ake wa lakabi da Three Lions, Thomas Tuchel, shi ma ya na sha’awar ya yi amfani da dan wasan mai buga gaba a matakin kasa.
- Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Legas, Mutane 10 Sun Kamu
- CMG Ya Nuna Fina-Finan “Documentary” Bisa Jigon “Kama Hanyar Samar Da Wadata”
Chelle ya shaida wa SCORENigeria cewa “A lokacin tafiyata zuwa Ingila (don ganawa da taurarin Nijeriya irin su Aled Iwobi da Wilfred Ndidi), na ce zan so Nwaneri ya buga wa Nijeriya wasa.”
“Saboda haka ina fatan hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) za ta yi magana da shi, sannan ni ma zan yi magana da shi, domin shawo kansa zai yi wahala saboda Ingila ma za ta so ta mayar da shi cikakken dan wasanta dake buga wasannin kasa da kasa, amma na yi imanin zan iya gamsar da shi saboda zan yi magana da shi game da yanayin wasan da kuma abin da ya dace bayan NFF ta tuntuve shi”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp