Tawagar Super Eagles ta yi maraba da hazikan yan wasanta biyu Ademola Lookman da Cyriel Dessers a sansaninsu na atisaye da ke Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom, gabanin fafatawar da za su yi a rukunin C a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2026 da kasashen Rwanda da Afirka ta Kudu.
Jami’in yada labarai na tawagar Super Eagles, Promise Efoghe ne ya sanar da zuwan yan wasan sansanin a ranar Laraba da yamma, a cewar Efoghe, a halin yanzu yan wasa 18 ne suka iso zuwa sansanin, inda ake sa ran karin yan wasa biyar za su shiga sahun nan gaba kadan wasannin.
Kwananan, Dessers ya kammala canza sheka zuwa kungiyar Rangers ta kasar Scotland daga Panathinaikos ta kasar Girka, hakazaika Lookman zai ci gaba da zama tare da Atalanta, saboda yunkurinsa na komawa Inter Milan bai yiwu ba, duk da rade-radin da ake yi na alakanta shi da zakarun Jamus Bayern Munich.
Super Eagles na shirin buga wasannin neman gurbin kofin Duniya, inda za su karbi bakuncin Rwanda a Uyo a ranar Asabar 6 ga watan Satumba, kafin su kara da Afirka ta Kudu bayan kwanaki uku, daga cikin yan wasan da ke sansanin a halin yanzu sun hada da Kyaftin Troost Ekong, Alex Iwobi, Wilfred Ndidi, da Moses Simon, sauran sune, Calvin Bassey, Fisayo Dele-Bashiru da Ola Aina da Bright Osayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp