A ranar Talata ne kasar Faransa ta samu tikitin buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya na matasa ‘yan kasa da shekaru 17 da ake yi a kasar Indonesia, bayan ta lallasa kasar Mali da ci 2-1.
Faransa na fatan lashe kofin a karo na biyu bayan nasarar da suka samu a shekarar 2001.
- Kofin Duniya Na Matasa ‘Yan Kasa Da Shekaru 17: Kasar Faransa Ta Tsallaka Zagayen Karshe
- Sin Ta Kammala Tsara Aikin Tauraron Dan Adam Mai Nisa Na Farko Domin Samar Da Hidimar Intanet Mai Inganci
Za su buga wasan karshe da kasar Jamus a ranar Asabar a birnin Javan na kasar Indonesia.
Jamus ta doke Argentina a daya wasan kusa da na karshe da ci 4-2 a bugun fenariti bayan da suka tashi 3-3.