Tawagar kwallon kafa ta matasa ‘yan kasa da shekaru 17 na kasar Moroko sun samu nasarar tsallakawa zuwa mataki mai kasashe 8 a gasar cin kofin Duniya na matasa ‘yan kasa da shekara 17 bayan doke kasar Iran a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Kwallayen da Ouazane, Azaouzi, Nasih da Zahouani suka zurawa kasar Iran yasa suka samu nasara akanta.
Yanzu Moroko za ta hadu da wata kasar Mali a wasa na gaba da za a buga ranar 25 ga watan Nuwamba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp