A kwanan baya ne ‘yan Nijeriya suka wayi gari suka ga darajar Naira ta sauka kasa saboda tashin farashin dala, inda hakan ya zamo babban abin damuwa ganin yadda takardar ta Naira ta sauka har zuwa 710.
Wannan kalubalen ya janyo shafar daukacin tattalin arzikin kasar nan, inda hakan ya haifar da hauhawan tashin farashin kayan masarufi, makamashi da kuma shafar fannin sufurin Jiragen sama.
Hakan ya kasance tamkar kamar na lokacin tsohon shugaban kasa na na mulkin soji Janar Badamasi Babangida da ya kirkiro da tsarin SAP wanda ake yi masa lakabi da aji a jika biyo bayan shiga cikin tsarin karbar lamunin IMF, inda masu nazari a fannin tattalin arziki suke ganin shine silar faduwar darajar Naira Da kima gazawar kula da jin dadi da walwalar ‘yan Nijeriya.
An dai takardama iri -iri, kan menene musabbabin da ke shafar kudaden musayar.
Bugu da kari, ta kasance kowa na dora wa juna laifi da kuma tunanin menene mafita don a sake dawo da darajar Naira a kasar nan wacce a shekarun baya da suka gabata, ana yin musayar ta a kan 85 dai dai takadar Pound.
A yanzu haka dai, kowa ya zura wa Babban Bankin Nijeriya CBN ido ganin cewa, Bankin shine ke da alhakkin samar da tsare-tsare da kuma sa ido kan yadda tafiyar da ayyukan musayar kudaden a kasuwar musayar kudaden domin ya tabbatar da cewa Naira ta samu dai daito.
Hakazalika, an yi yunkuri wajen kawar da kai kan maganar da take a zahirance na cewa kudaden waje ko wadanne iri ne, ana samun su ne ta hanyar zage wa wannan takardamar ta zama wajibi a mayar da hankali wajen a tattauna kan yadda za a sake farfado da darajar Naira a Nijeriya ta hanyar samar da tsare -tsare.
Kamfanin mai na Shell a kwanan baya ya bayyna cewa, abin takaici, Nijeriya ta ci gaba da kasance wa kasa da ta dogara kachokam a kan man Fetur da iskar Gas, inda kuma bata gari ke kutsa wa a cikin fannin suna sace man da aka samar da ya kai kusan kashi 80 a cikin dari, inda kuma ake ci gaba da samun tashin farashin gangar mai a kasuwar duniya.
Bisa da wannan fahimtar, zai iya tuna wa hakan ne ya sa bayan da makuntan CBN na yanzu suka shiga ofishi ne, suka kirkiro da sabbin tsare-tsare don a farfado da tattalin arzikin kasar nan yadda za a kara fadada samar wa da Nijeriya hada-hadar kudaden musaya na ketare.
Namjin kokarin da CBN ya yi wajen wanzar da wadannan tsare-tsaren sun taimaka matuka wajen sake farfado da fannin ayyukan noma musamman a karkashin shirin aikin noma Anchor Borrowers da kuma samar da tsarin yin noma don Ribas wadanda suka kasance daya daga ciikin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Bugu da kari, a cikin tsarin, CBN ya haramta shigo da kayayyaki 43 daga ketare tare da rage harkallar kasuwar fage ta musayar kudade wanda duk anyi wannan ne, don a magance kalubalen samar da kudaden musaya a kasar.
CBN ya kuma mayar da hankali a kan fannin da bai shafi harkar mai ba kamar fannin hakar ma’adanai, inda bankin ya zuba kudade a fannin don habaka sarrafa kayan da ake sarrafa wa a cikin gida Nijeriya, musamman domin a rage shigo da kaya daga ketare, musamman domin a habaka samar da kudaden musaya a kasar.
Har ila yau, bisa wasu alkaluman da CBN ya fitar sun nuna cewa, fannin ilimin boko na kasar nan ya fuskanci barazana sama da shekaru goma da suka wuce inda kuma a wata kididdigar ta CBN ta nuna cewa, Nijeriya ta kashe makudan kudade har dala biliyan 28.65 a cikin shekaru goma wajen zuwa neman ilimin boko a kasar waje wato daga 2010 zuwa 2020 duk wadannan dimbin kudaden ana samar da su ne ta hanyar kudaden musaya na kasar waje.
Har ila yau, abinda ke kara ciwa CBN da tattalin arzikin Nijeriya Tuwo a Kwarya shine, akasarin wadannan kudaden na musayar da ake yin amfani da su, na jabu ne domin an samo su ne a kasuwar bayan fage.
Bugu da kari, an kiyasta cewa, Nijeriya na tabka asarar da ta kai ta kimanin dala biliyan 1.3 a duk shekara wajen fitar da ake yi daga kasar zuwa ketare domin neman lafiya, inda hakan ya zamo wani babban nauyi a kan tattalin arzikin kasar.
Karin wani abin tkkaci shine, yadda kasuwar bayan fage a kasar ta koma tamkar ita ce ke jan Akalar kasuwar musayar kudaden musaya na kasar waje.
Yanzu Nijeriya na tunkarar kakar zaben 2023, inda kuma ‘yan siyasa a kasar ke ta kai Gwaro da Mari wajen samo kudaden musaya na kasar waje don fara gabatar da yakin neman zabe.
Anga irin wannan yar manuniyar a yayin da wasu jamiyyun siyasa a kasar suka yi ta ruwan dala a lokacin gudanar da zaben fidda gwani a kwanan baya, inda hakan ya kara shafar tattalin arzikin Nijeriya.
Wasu masu fashin baki na da ra’ayi wanda nima shine nawa irin ra’ayin cewar, mafita ita ce Gwamnatin Tarayya ta hanyar yin amfani da CBN ba tare da bata wani lokaci ba, ta daina samar da rangwame a fannonin kiwon lafiya da ilimin boko kuma Gwamnatin ta kara sanya wadannan fanonin biyu, a cikin kayayyaki 43 da aka haramta shigo wa da su cikin kasar nan.
Ya kamata CBN ya kara matsa lamba a Kan masu samar da kudaden musaya na kasar waje a kasar nan da kuma magance masu janyo kalubale a fannin
Ina da yakinin cewa, matukar aka rungumi tare da kuma wanzar da wadannan matakan, za su bai wa kudaden musaya na kasar waje damar kara daga darajar Naira.
Akwai kuma bukatar Gwamnatin ta kara jajirce wa wajen kara bai wa CBN kwarin gwiwar don gudanar da ayyukan da ya sa a gaba.
Adegoke, mai fashin baki ne a kan alamuran yau da kullum kuma ya na da zama a garin Akure a jihar Ondo.