• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kokarin Farfado Da Ilimi: Gwamnan Kano Ya Zama Gwarzo A Tsakanin Gwamnoni

byAbdullahi Muh'd Sheka
12 months ago
Ilimi

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na ci gaba da karbar gwababan lambobin yabo wadda ke alamta nagarta da jajircewarsa wajen bunkasa harkokin ilimi da tsantsenin lalitar al’ummar Kano inda wannan ne babban dalilin da Kanawa ke kiransa da sunan “A kori jahilci”.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na cikin gwamnoni shida da suka rabauta da babbar lambar yabo daga kungiyar Malamai ta Kasa tare da hadin guiwa da ma’aikatar ilimi ta Tarayya a lokacin bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a babban filin taron Eagle Skuare da ke Abuja.

  • Hadarin Kwale-kwale A Kaiama: Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 100
  • Ba Mijina Ba Ne Sanadin Ƙuncin Rayuwa Da Ake Ciki A Nijeriya – Uwargidan Shugaban Ƙasa

Inda aka karrama Gwamna Abba da lamba mafi daraja bisa kyakkyawar nasarar da ya samu ta fuskar inganta harkar ilimi. Kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa

Jajircewa tare da sadaukar da kan Gwamna Abba ne ya ja hankalin kungiyar Malaman tare da hadin guiwar Ma’aikatar ilimi ta tarayya wajen zabo shi domin ba shi wannan lamba musamman matakinsa na Sanya wa harkar ilimi dokar ta-baci tare da kafa manyan kwamitoci domin magance matsalar da ta jima tana ci wa harkar ilimi a tuwo a kwarya a Kano. Musamman tsarin tallafa wa malamai tare da kyautata walwalarsu.

Wani abu da ke daukar hankalin duk wani mai rajin kishin ganin an farfado da harkar ilimi a Kano shi ne yadda gwamnan bai tsaya ilimin zamani ba kawai, har makarantun tsangayu da islamiyyu ya saka cikin jadawalin inganta harkar ilimin baki daya.

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Domin ganin aniyarsa ta sake farfado da harkar ilimi ta kai inda yake fata, Gwamna Abba a kasafin kudin wannan shekara ta 2024, ya tabbatar da gabib sashin ilimi ne ya rabauta da kaso mafi tsoka domin tabbatar da cimma nasara. Musamman shirinsa na kara gina ajujuwa, zuba kayan zama da raba kayan koyo da koyarwa ga daukacin makarantun Jihar Kano.

Irin wadannan ayyuka ne Gwamna Abba ya alkawarta wa Kanawa kuma gashi tun kafin a yi rabin wa’adi kwalliya tana biya kudin sabulu.

A halin da ake ciki, tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran Jam’iyyar NNPPFormer, Rabi’u Musa Kwankwaso ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar samun lambar yabo mafi daraja daga Kungiyar Malaman Makaranta ta Kasa (NUT), bisa hobbasar da yake yi wajen bunkasa sashen ilimi.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a shafinsa na D (da aka fi sani da Twitter a baya), inda ya nunar da cewa hakika, Gwamna Abba ya nuna sadaukarwa ga farfado da sashen ilimi na Jihar Kano inda ya bukaci ya kara kaimi a kan hakan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version