El-Zaharadeen Umar" />

Kokarin Hana Bara: Mu Ma Almajirai Ne..!(2)

A satin da ya gabata na yi alkawari cewa zan cigaba da wannan rubutu domin kara bayyana matsayi da daraja tare da girma irin da almajiran da gwamnatin tarayya take son ganin bayansu bayan ta ci amfaninsu.

Da yardar Allah a wannan makon zan bayyana wadanda suka yi nasara a wannan harka ta almajiranci wanda har yanzu suna cikinta kuma ita suka dogara kuma nan ne hanyar cin abinci.

Kowa ya sani, duk lokacin da wani abu ya taso, sai ‘yan siyasa musamman idan batun ya shafi neman duniya ko wata nasara ta neman mukami ko kauda wani daga inda yake, to har gobe malamai almajirai suna taka mahimmiyar rawa wajan faruwar hakan acikin al’umma.

Babu wani dan siyasa ko mai neman mulki da baya da malami wanda asasin shi wannan Malami shi ne almajiranci, kamar yadda na fada a satin da ya gabata kowane irin aiki da hulda tana da nata mahimmanci da kuma akasin haka.

A bisa wannan dalili yasa kowane dan siyasa yana da Malami (Almajiri) wannan kalma ta almajiri tana da matukar tasiri da mahimmacin a tsakanin almajirai domin kuwa duk girman Malami idan zai hadu da dan uwansa Malami (Almajiri) ma damar zai gaisa da shi gaisuwa irin ta girmamawa sai dai kaji Malamin (Almajiri) yana cewa Almajiri dai “Akaramukallah”

Duk dan siyasar da yake neman wani abu ko wanene shi a duniyar siyasar arewacin Najeriya sai ya yi hulda da almajirai, ashe ke nan idan har aka hana wannan tsari muna iya cewa ‘yan siyasar arewa sun shiga shida, saboda idan muka duba a zahiri shugaba Buhari da yake ta wannan kokari na hana bara, to ya fada cewa ba zai sake tsayawa takara ba, wannan ya nuna cewa amfanin Malami (Almajiri) ya kare a wajansa saboda haka yana da yadda zai yi maganinsa bayan ya gama cin amfaninsa kafin ya zama shugaban kasa.

Mutane da dama za su yi mamaki idan aka  ce shugaba Muhammadu Buhari yana da Malami (Almajiri) amma ya koma daga gefe guda yake son ya ci mutuncinsu da sunan matsalar tsaro, ni ina ganin kamata ya yi ace ya neme su domin jin wacce irin shawara za su bada wajan maganin matsalar tsaron da ta gagari gwamnatinsa ana ji ana gani amma ya like akan mulki.

Idan muka koma batun mutane da suka samu nasara a rayuwa ta hanyar almajiranci akwai shehunai irin su Maulana Sheihk Dahiru Usman Bauchi, ko yanzu da wannan batu ya so, ya yi magana inda ya bayyana cewa sai dai Buhari ya yi duk abinda zai yi, amma maganar hana almajiranci ya kyale wannan batun domin kuwa ba abu ne mai zai yuwo ba.

Duk mutumin da zai rabi mutane irin su Sheikh Dahiru Usman Bauchi zai kara gane manufar Buhari akan almajiranci domin ta wannan hanyar an samar da al’umma ingantacciya wanda zata dawwama cikin nagarta a dalili wannan hanyar ta almajiranci.

Mahaddata alkur’ani da wannan hanyar ta samar kuma al’umma take cin amfaninta ba su da iyaka, matasan da suka samu shiriya ta wannan hanyar sun dauki kashi mai tsoka a cikin al’ummar Hausawa wanda a dalilin haka gwamnatin bata san da matsalarsu ba.

Muna iya cewa da ba dan wannan hanyar ta almajiranci ba da yanzu gwamnati da sauran hukumomi suna nan suna fama da wata matsalar bayan wacce ta addabi su ta shaye-shaye da wasu matasan ke yi amma sunki yin karatun Allo domin kada ce masu almajirai.

Ina da wannan tabbacin kafin ka samu mutun wanda ya bi hanyar almajiranci tsakaninsa da Allah kuma ka samu shi yana aikata wani abu makamanci halaryar ‘yan Boko ta shaye-shaye gaskiya da wahala, amma kowa yana ganin yadda ‘ya ‘yan masu gudun almajirai da bakin sun koma manya mashaya an rasa yadda za ayi da su a wannan kasa.

Haba Malam, ga aiki nan a gaban wannan gwamnagti sai kawai saboda daukar hankalin jama’a ta jawo masu wata sabuwar fitina, sai kawai ace wai za a hana harkar almajiranci saboda tsabar kin Allah kai Buhari ka sake tunani, nan dai kam bida ta ga rana.

Kazalika idan muka sake yin duba da manyan Malamanmu wadanda har gobe duk da cewa sun rasu amma sun zama jigo sun kuma kafa tarihi kafin su bar wannan duniya ta wannan hanya ta almajiranci.

Mutane irin su Sheihk Isiyaka Rabi’u har gobe kamar suna raye a dalilin wannan hanya, kuma a lokacin da suke cikin wannan harka ta almajiranci babu wani tsageran dan siyasa da giyar mulki ta huda da zai kuma daga baya ya ce na hana wannan harka ta almajiranci.

Wadannan mutanen har duniya ta kare ana cin gajiyar abinda suka bari wanda ya samu ne ta wannan hanya da mai mulkin karshen zamani zai ce wannan matsalar tsaro tana da alaka da almajiranci kuma ya kasa banbance wane irin almajiranci wanda jama’a suka tsinci kansu a dalilin mulkisa ko ko wanda jama’a ke yi domin samun abin sawa a bakin sati, ko kuma yana nufin almajirai masu yin bara domin samun damar karatun alkur’ani mai girma?

Har gobe babu cikakkiyar amsa akan wane irin almajiranci ne yake nufi yana da alaka da matsalar tsaron ake tunanin shine ya nadota cikin sha’anin rashin iya shugabanci, ‘yan bindiga suna ta kashe al’ummomi musamman a jiharsa ta Katsina da Zamfara amma shi ba wannan bane ya dame shi ba, a’a masu yin bara suna samun abinci suna karanta alkur’ani sune manyan masu matsalar a wajansa.

Haka kuma idan muka koma baya zamu iya gane irin yadda ‘yan siyasa ke wasa da hankalin jama’a kowa ya sani yanzu wani sabon salon da ‘yan siyasa ke amfani da shi duk Malamin (Almajiri) da aka ce ya iya aikin rokon Allah yanzu zaka ga wani shakiyin dan siyasa ya dauke shi ya maida shi gidansa da ke Abuja ko kuma ya rika turashi zuwa kasar Saudiya domin rokon Allah akan bukatarsa ta duniya.

Wannan ke sa ga ji almajirai na cigiyar malaminsu saboda ya kwana biyu baya nan, ada ‘yan siyasa suna zuwa wajan Malamai (Almajirai) a boye domin kadda jama’a su gansu a rika ce masu mushirikai yanzu kuwa sun sha ta dubu komi za a ce an dade ba a ce ba, indai akan wannan harka ne a shirye suke a gansu wajan (Almajiri) tare da jami’an tsaro suna yi masu rakiya.

A jihar Katsina anyi wani malami (Almajiri) da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida yake wanko kafa daga Lagas ko Abuja ko kuma MInna ya zo wajansa domin dai kawai yasan girma da kima tare da darajar Malam (Almajiri) kuma ba shi kadai ba, ku duba duk sauran ‘yan siyasar kowa yana da na shi wasu sun boye ne wasu kuma a fili suke nunawa.

Haka kuma nasan wani dan siyasa a nan Katsina duk lokacin da harkar zabe ta karato yana dauko malamansa (Almajirai) ya kai wani gidansa a cigaba da yin karatu alkur’ani da almajirai suka samu ta wannan hanya ta almajiranci, amma kawai sai a bushi iskar mulki a ce bara bata da ce da wannan kasar ba, to halin da ka jefa wannan kasa ai mun godewa Allah da abin ya tsaye iya barar.

Sannan idan muka duba anan kusa-kusa zamu ga cewa tsohon shugaban gidan Radiyon Tarayya FRCN a lokacin tsohuwar gwamnatin Dakta Ladan Salihu asalinsa almajiri ne, amma cikin ikon Allah duba abinda ya zama sannan ina da tabbacin mutane irin su Ladan Salihu ba za su taba sukar almajiranci ba har abada.

Har yanzu nan da nake wannan rubutu ana damawa da su a ciki  harkokin gwamnati amma yanzu a matakin jiha bayan an dama da shi a tarayya, almajiri bawan Allah. Idan Allah Ya kaimu sati mai zuwa zan cigaba zaku kara jin wasu mutanen da suka yi nasara ta wannan hanya. Sannan za a ga irin yadda wasu gwamnoni suka dauki wannan bangare da mahimmaci inda har suke bada mukamin mai bada shawara akan harkokin almajirai.

Exit mobile version