Yuwancin jihohin kasar nan da Allah ya albarkata da dimbin ma’adanai daban-daban sun kasa fito da hanyoyin cin gajiyarsu ta yadda al’umma jihohin za su amfana.
Masana nada ra’ayin cewa, in har da za a tatsi wadannan ma’adanai yadda ya kamata lallai zai taimaka wajen bunkaska tattalin al’umma ya kuma rage yadda jihohi ke dogaro da kudaden da gwamnatin tarayya kr rarraba musu daga asusu arzikin kasa, wanda da hakan ya bayar da damar gudanar da ayyukan ci gaban al’umma a cikin sauki.
- DSS Sun Cafke Dan Jarida A Filin Jirgin Sama Akan Hanyarsa Ta Zuwa Umrah Daga Kano
- Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke
A tsawon shekaru, gwamnatocin jihohi suna kokawa a kan yadda wasu dokoki suke takura musu amfana daga albarkatun ma’adanmai da k ea jihohin nasu, musamman dokar da ta bai wa gwamnatin tarayya mallakin albarkatun kasa a duk inda suke a fadin tarayyar kasar nan.
Kudin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 (wadda aka yi wa kwaskwarima), sashi na 44 (3) banagare na 39 ta bai wa gamnatin tarayya mallakin dukkan albarkatun kasa don ta yi amfani da su wajen inganta rayuwar al’umma.
Haka kuma dokar ma’adanai da hakarsa ta Nijeriya na shekarar 2007 a sashi na 1 (1) ya kara tabbatar da mallakar dukkan ma’adanai a fadin tarayyar kasar nan a matsayin mallakin gwamnatin tarayya.
Bincike ya nuna cewa a halin yanzu harkar hakar ma’adanai ba bisa ka’dida ba ya zama ruwan dare, lallai a kwai bukatar gwamnati a dukkan matakai su hada hannu don kawo karshen harkokin ‘yan kasashen waje wadanda suke hada baki na wasu bata gari a cikin shugabannin al’umma wajen sace albarkatun kasa.
Ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba na faruwa ne a daidai lokacin da al’ummar jihohi ke rayuwa cikin matsanancin talauci, an kuma tabbatar da cewaa, harkar hakar ma’adanai na ta’azzara matsalar tsaro da ake fama da shi a cikin kasa da kasashe makwabta.
A Jihar Kaduna, Kamfanin Bunkasa harkokin Ma’adanai ‘Kaduna Mining Debelopment Company Limited’ ta ba kamfanoni 30 lasisin gudanar da harkokin hakar ma’adanai a fadin jihar, wadanda suka hada da lasisi 11 na masu hakar duwatsu da lasisi 21 na masu nema tare da hakar ma’adanai da suka hada da ‘Granite, Laterite, Gold, Tin, Columbite, Tantalite, Iron, Manganese, Garnet, Beryllium, Nickel, Platinum, Cobalt da Lithium a kananan hukumomi daban-daban a fadin jihar.
Sauran ma’adanan da ke samu a jihar Kaduna sun hada da ‘Cassiterite (tin-ore) a garin Kagoro da ke karamar hukumar Kaura da Kurmin Dangana a karamar hukumar Jaba, haka kuma ana samun Tantalite a kananan hukumomin Birnin Gwari, Kagoma, Kafanchan da sauran sassan jihar.
A na samun Columbite a Jema’a, Ikara, Sanga da karamar hukumar Jaba wanda ma’adanan suna da muhimmanci a wajen hada jirgin saman da wasu na’urori masu muhimmanci. Ma’adanin Bismuth da ake amfani da shi a masana’antar hada magunguna yana samuwa ne a yankin garuruwan Gimba da Kinkiba a karamar hukumar Soba da kuma Makarfi a karamar hukumar Makarfi. Haka kuma ana samun ‘Wolframite a yankin Banki da Tsaunin Giniya; Gwal kuma na shinfide a yankin Birnin Gwari, Giwa, da karamar hukumar Chikun; ana kuma samun ma’adanin Nickel a kauyen Dangoma da ke karamar hukumar Jema’a; yayin da ma’adanin ‘Gemstones, Amethyst, Akuamarine da Tourmaline ke shinfide a kusan dukkan kananan hukumomin jihar.
A ta bakin shugaban hukumar kula da harkokin ma’adanai ta Jihar Kaduna, Dakta Nura Sani, ya bayyana cewa, jihar na da albakatun ma’adana masu dinbin yawa kuma jihar ta kasance a kan gaba a bangaren mallakar ma’adanai a cikin jihohin kasar nan.
Ya kara da cewa, an yi fiye da shekara 100 ana harkokin hakar ma’adanbin Gwal a yankin Birnin Gwari. Ya ce, ana hakar ma’adin karfe a yankin kudancin Kaduna, Kubau da Lere.
Ya ce, jihar ta hada hannu da wasu kamfanonin hakar ma’adanai na kasashen waje inda suka zuba jarin fiye da Dala miliyan 600 don kafa kamfanin hakar ma’anin karfe a karamar hukumar Kagarko.
Ya kuma kara da cewa, jihar na a kan gaba a harkar ma’adanin ‘Lithium’ inda suka hada hannun da wani kamfanin kasa Sin a don hakar ma’adanin a kauyen Kangimi da kuma wani hadin gwiwar da kasar Australian a hakar ma’adanin ‘Jubita’.
Ya kuma kara da cewa a halin yanzau Jihar Kaduna ta zama kan gaba a harkokin hakar ma’adanin “Gemstones’ da “Safayers” ana kuma shirin ganin gwamnati ta zuba jari don ganin al’ummun yankin sun amfana yadda ya kamata.
“Jihar Kaduna da shirya tsaf don samar da hanyoyin amfana daga ma’adanai masu muhimmanci da Allah ya albarkaci jiharmu da su, kamar ‘Amethyst a yankin Ikara, da “Lithium, a yankin Kurega da Manini. Haka kuma kamfanonin kasa Hong Kong sun shigo don hada hannun da mu a bangaren hakar ma’adanin “Tin mining’ a garin Gidan Waya da ke karamar hukumar Jema’a.” in ji shi.