A ranar 10 ga watan nan, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da shirin kafa yankin kare muhallin halittu a Tsibirin Huangyan. Wannan shiri ya kasance karin mataki da Sin take dauka na kare muhallin teku da ke kewaye da tsibirin. Amma ma’aikatar harkokin wajen Philippines ta bayyana “korafi mai karfi” game da hakan. Wani manazarci na ganin cewa babu ruwan Philippines kan matakan da Sin ta dauka a yankinta.
Philippines ta dade tana yunkurin neman mamaye Tsibirin Huangyan. “Korafin” da ta yi ya tabbatar da cewa matakan da Sin ta dauka sun dace kuma suna karkashin doka, wanda ke nuna alhakin Sin na mayar da tekun Kudancin Sin ta zama wurin zaman lafiya, abota da hadin gwiwa.
- Kasar Sin Daya Ce Daga Cikin Kasashen Duniya Da Aka Amince Da Su a Matsayin Mafi Zaman Lafya
- Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur
Tsibirin Huangyan, a matsayinsa na babban tsibirin teku, muhallinsa babu inganci. Matakan da Sin ta dauka sun dace da yarjejeniyar MDD kan dokar teku da sauran dokokin kasa da kasa.
Bugu da kari, kafa wurin kare muhalli na kasa da kuma tsara ayyukan kamun kifi a tekun tsibirin Huangyan na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antar kamun kifi a yankin.
Matakin da Sin ke dauka a wannan karo ya nuna iyakoki da manufofin da aka tsara a karkashin doka, ya kuma fayyace iyakokin ayyukan da suka kamata a yi a tekun tsibirin Huangyan, kana ya bullo da shiri mai ma’ana domin rigakafin barkewar rikice-rikice. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp