Babbar Kotun Jihar Legas ta ƙi amincewa da buƙatar Godwin Emefiele, tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), na dakatar da shari’ar da ake yi masa kan zargin cin zarafin ofis.
Mai shari’a Rahman Oshodi ya yanke hukuncin cewa kotun na da iko da shari’ar da ake masa.
- Kotu Ta Ƙi Amicewa Da Dakatar Da Shari’ar Emefiele
- Yarinyar Da Ake Zargi Da Zuba Wa Mijinta Da Abokansa Guba A Abinci, Ta Amsa Laifinta A Kotu
Sai dai, ya yi watsi da zarge-zargen huɗu saboda ba su dace da doka ba.
Emefiele, tare da wanda ake tuhuma Herry Omoile, na fuskantar zarge-zargen cin hanci, karɓar rashawa da kuma zargin mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida.
Emefiele ya ƙalubalanci cewa kotun ba ta da hurumin sauraren shari’arsa, yana mai cewa matsayinsa na gwamnan CBN yana nufin ba zai iya fuskantar shari’a a kotun Jiha ba.
Sai dai Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ƙalubalanci hakan, inda ta ce kotun na da hurumin sauraren ƙarar.
Hukuncin mai shari’a ya mayar da hankali ne kan batun iko kawai, ba tare da duba ainihin zarge-zargen ba.
An ɗage shari’ar zuwa 24 da 26 ga watan Fabrairu don ci gaba da sauraron shari’a.