Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar.
Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello.
- An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo
- Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57
Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya Bello daga gwamnatin jihar Kogi ko wata ƙaramar hukuma zuwa asusun makarantar AISA ba, ya kuma karanta wani ɓangare na hukuncin da kotun FCT ta yanke cewa babu umarnin kotu da ya umarci makarantar AISA da ta mayar da kuɗaɗen zuwa hukumar EFCC.
Al’ƙalin ya yanke shawarar ɗage shari’ar don yanke hukunci kan bukatar EFCC ta yi wa shaidar tambayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp