Kotun majistare ta daya da ke Sakkwato a ranar Litinin ta tura mataimaki na musamman ga Sanata Aminu Waziri Tambuwal, mai suna Shafi’u Umar Tureta gidan gyaran hali kan yada bidiyon matar Gwamna Ahmed Aliyu a yayin da ake yi mata liki da dala.
Mai shari’a Fatima Hassan ce ta yanke hukuncin tsare matashin mai shekaru 36 har zuwa ranar 6 ga Satumba inda za a yanke hukunci kan yiwuwar bayar da belinsa kan laifin batancin. Sai dai kuma, an hana manema labarai halartar zaman kotun a yayin yanke hukuncin na farko.
- Abba Ya Gabatar Da Kwarya-kwaryar Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 99 Ga Majalisar Kano
- A Shirye Sin Take Ta Ci Gaba Da Yin Hadin Gwiwa Tare Da Kasashen Afirka Wajen Sa Kaimi Ga Inganta Shirin Rage Talauci
Takardar shigar da karar ta bayyana cewa, matashin a ranar 18/7/2023 ya yada bidiyon matar Gwamna, Fatima Ahmed Aliyu a yayin da take bikin zagayowar ranar haihuwarta, sannan ya kara da cewa, ta na almubbazaranci da liki da kashe kudade a yayin da al’umma ke cikin yunwa.
Bugu da kari, ana tuhumar matashin da laifin sanya tsohuwar takardar kammala makarantar sakandiren Gwamna Aliyu da sakamakon gazawa (F9) tare da kiran sa bakauye wanda bai iya magana da turanci ba, laifukan da dansanda mai shigar da kara, Abdurrahman Mansur ya ce, sun sabawa kundin dokar penal code ta jihar ta 2019 sashe na 378 da 379.
Sai dai jam’iyyar PDP a jihar, ta bukaci a gaggauta sakin matashin, inda ta ce, ba Shafi’u ne ya dauki bidiyon da Gwamnan ke turancin ba, saboda ba shi da wata alaka ta shiga gidan gwamnati inda aka dauki bidiyon, haka kuma, bai halarci wurin bikin zagayowar ranar haihuwar matar gwamnan ba, don haka, ba inda zai samu bidiyoyin sai ta hanyar makusantan gwamnan da iyalansa da suka yada.
Kakakin jam’iyyar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya bayyana cewar, mulkin kama-karya ne gwamnatin Sakkwato ke yi tare da kokarin cin zarafin ‘yan adawa ko ‘yan PDP, domin hakan rashin adalci ne kuma ba za su zuba ido a na cin zarafin magoya bayan su ba.
A nata bangaren, kungiyar kare hakkin dan’Adam ta ‘Amnesty International’ ta bi sahun wadanda suka soki lamarin, inda ta ce, kama matashin ya sabawa ‘yancin dan’Adam, don haka, ta yi Allah-wadai da kamen tare da kiran a gaggauta sakinsa.
Kungiyar ta ce, maimakon kama matashin, kamata ya yi, gwamnatin ta bayar da fifiko ga magance matsalolin fatara, yaran da ba su zuwa makaranta da ke gararanba kan tituna da yawaitar matsalar tsaro da ta kassara gabashin jihar.