Wata babbar kotu dake zaune a jihar Kano ta yanke wa wani kocin kwallon kafa mai suna Hayatu Muhammad hukuncin daurin shekaru 8 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba bisa laifin yin luwaɗi da wani dan wasansa da bai kai shekara takwas ba.
Alƙalin kotun mai shari’a Musa Dahuri Muhammad na babbar kotun jihar Kano da ke kan titin Miller ne ya zartar da hukuncin bayan ya samu kocin da laifuffuka biyu na lalata da karamin yaron a wurare daban-daban a jihar.
A cewar mai gabatar da kara na jihar, Barista Ibrahim Arif Garba, wanda aka yankewa hukuncin, mazaunin unguwar Sanka ne a Kano, an gurfanar da shi ne bayan bincike ya tabbatar da faruwar lamarin, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu biyu wadanda shaidarsu ta gamsar da kotun cewa kocin ya aikata laifin.
A yayin shari’ar, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da shaida wadda ta gamsar da ita ba tare da wata shakka ba. Mai shari’a Dahiru ya ce laifin ya ci karo da sashe na 284 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta yin jima’i ba bisa ka’ida ba, don haka ya yanke wa Hayatu Muhammad hukuncin daurin shekaru hudu a kan kowanne daga cikin tuhumomin biyu, wanda zai fara ne tun ranar da aka kama shi.