Wata kotun majistare da ke Rijiyar Zaki a Jihar Kano, ta yanke wa wani mutum, Alhaji Inuwa Ayuba, hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu bayan samun sa da laifin sare bishiya guda bakwai ba tare da izini ba a ƙauyen Sarauniya, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Lauyar da ke gabatar da ƙara, Barrista Bahijja Aliyu, ta shaida wa kotu cewa Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta samu labarin sare itatuwan ta hanyar bayanan sirri, inda tawagar sa ido ta je ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da tattara hujjoji masu ƙarfi.
- Nazari Kan Amfanin Noman Kanumfari
- Yanzu Ne Lokacin Da Arsenal Ya Kamata Ta Lashe Kofin Zakarun Turai – Walcott
Ta bayyana cewa dokokin muhalli na Jihar Kano sun hana sare bishiya ba tare da samun izini daga hukumomi ba, domin tana ƙoƙarin daƙile gurɓatar muhalli da kuma kawar da bayan gida a fili.
Bayan nazarin shaidun, kotun ta same shi da laifi, inda ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na wata biyu tare da zaɓin biyan tara.
Haka kuma, kotun ta umarce shi da ya dasa sabbin bishiyoyi guda 14 a matsayin diyya.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Hashim, ya yaba wa tawagar sa ido da kuma kotu kan yadda suka jajirce wajen kare muhalli.
“Wannan hukuncin zai zama izina ga sauran mutane da ke aikata laifukan da ke cutar da muhalli.
“Za mu ci gaba da aiki tuƙuru wajen kare albarkatunmu don amfanin wannan zamani da na gaba,” in ji Dakta Hashim.
Haka kuma, Daraktan Wayar da Kai na ma’aikatar, Ismail Gwammaja, ya buƙaci jama’a da su kiyaye dokokin muhalli tare da sanar da hukumomi duk wani laifi da ke cutar da muhalli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp